logo

HAUSA

Ismael Inoussa Ali: Ina fatan ganin karin ‘yan Nijar su zo kasar Sin yin karatu

2023-06-20 15:17:17 CMG Hausa

Ismael Inoussa Ali, dan Jamhuriyar Nijar ne, wanda a yanzu haka yake karatun digiri na farko a fannin kasuwancin kasa da kasa, wato International Trade a turance, a jami’ar Hebei dake birnin Baoding na lardin Hebei dake arewacin kasar Sin.

A zantawar sa da Murtala Zhang, malam Ismael Inoussa Ali ya bayyana dalilin da ya ba shi sha’awar zuwa kasar Sin don yin karatu, da yadda yake mu’amala da mutanen kasar, inda kuma a cewar sa, akwai zumunci da kyakkyawar alaka tsakanin sa da abokan karatun sa ‘yan China.

Malam Ismael yana kuma son ya taimaka wajen inganta hadin-gwiwa da kara fahimtar juna tsakanin mutanen Nijar da Sin, inda ya bayyana fatan sa, na ganin karin matasan Nijar sun samu damar yin karatu a kasar Sin, ta yadda za su iya yin amfani da abubuwan da suka koya a China, don gina kasar su wato Jamhuriyar Nijar. (Murtala Zhang)