logo

HAUSA

Ci gaban kasar Sin dama ce ba kalubale ba

2023-06-20 15:05:02 CMG Hausa

Kalaman shugaban kasar Sin Xi Jinping, yayin da yake zantawa da sakataren harkokin wajen Amurka dake ziyara a kasar Sin Anthony Blinke, sun bayyana wasu muhimman batutuwan jan hankali ga Amurka.

Zan iya cewa kalaman wata manuniya ce ga Amurka cewa, hanyar da ta dauka ba za ta bulle ba, kana jan hankali ne gare ta ta gyara kura-kuranta.

A cewar Shugaba Xi, takarar manyan kasashen duniya ba ta wakiltar yanayin da ake ciki, hakan kuma ba zai taba iya magance matsalolin Amurka ko  kalubalen da duniya ke fuskanta ba. Tabbas bai kamata yayin da ake fuskantar kalubale masu tsanani a duniya, babbar kasa kamar Amurka ta rika mayar da hankali kan takara ko yada jita-jita ba. Babu abun da wadannan abubuwa za su haifar face kara tada hankalin duniya da ta’azzara matsalolin da ake fuskanta.

Amurka ta kasance mai yin amai, kuma ta lashe. Ta kan nace cewa ba ta neman takara da kasar Sin ko kuma ba ta goyon bayan ’yancin yankin Taiwan na kasar, sai dai ayyukanta na yin hannun riga da abubuwan da take furtawa. A halin da ake ciki, duniya na bukatar Amurka mai sanin ya kamata da cika alkawarin da ta dauka da dakatar da kirkiro matsaloli ko ma kokarin karkatar da hankalin duniya daga yanayin da ake ciki.

A kalaman shugaba Xi, ya kamata kasashen su girmama muradun kowannensu, haka kuma, nasarorin da za su samu, dama ce maimakon barazana.  Har kullum burin kasar Sin shi ne ganin ci gaban kasashe, yayin da Amurka ke daukar hakan a matsayin barazana.

Doka ta ba kowacce kasa damar samun ci gaba, don haka, bai kamata wata kasa taya tilo ta kasance mai babakere ko bayar da izinin samun ci gaba ga sauran kasashe ba. Misali, kasar Sin ta samu ci gaba ne bisa jajircewarta, da hikimomi da basirar al’ummarta da ma tsarin shugabanci na kwarai, don haka babu wata kasa dake da izini ko damar iyakancewa ko kayyade ci gabanta. Ya dace Amurka da kawayenta su sakar ma Sin da ma sauran kasashe mara, su raya kansu ta yadda suke ganin ya fi dacewa da yanayinsu. Wannan a ganina, shi zai kai duniya ga samun ci gaba har ma da zaman lafiya. Kai ya riga ya waye, manufofin kasar Sin sun bambanta da na kasashen yamma, karfin kasar Sin ba ya nufin za ta yi wa duniya babakere. Har ila yau, ci gaban kasar Sin na zama dama ne ga kasashe masu burin raya kansu, Amurka da kanta na iya amfana daga hakan idan ta sauke girman kai da neman babakere.

Duk da kalubalen dake akwai da ma dimbin banbance-bambance, a matsayinsu na manyan kasashe dake zama abun koyi ga kasashe masu tasowa, har yanzu lokaci bai kurewa Sin da Amurka ba na lalubo hanyoyin inganta dangankarsu ko da kuwa za su yi hakan ne a hankali. Duniya na bukatar hadin kansu, duba da kasancewarsu manya, dama tasirin da Sin ke da shi tsakanin kasashe masu tasowa mafi rinjaye, don haka ya dace su yi la’akari da hakan don tabbatar da zaman lafiya da dunkulewar da ake muradi  a duniya. (Faeza Mustapha)