logo

HAUSA

“Zaman lafiya ta hanyar tattaunawa” ita ce kawai mafita ga Gabas ta Tsakiya

2023-06-19 18:41:54 CMG Hausa

A ranar 14 ga watan Yuni, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas a nan birnin Beijing. Sun sanar da kulla dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Falasdinu.

Shugaba Xi ya gabatar da shawarwari mai kunshe da abubuwa uku na warware batun Falasdinu. Ya bayyana cewa babbar hanyar warware batun Falasdinawa ita ce kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta wacce ke da cikakken ikon mallakar kai a bisa yarjejeniyar kan iyakoki ta shekarar 1967 da kuma gabashin Kudus a matsayin babban birninta. Ya kamata a biya bukatun tattalin arziki da rayuwar Falasdinawa, sannan kasashen duniya su kara kaimi wajen taimakon raya kasa da taimakon jin kai ga Falasdinu. Kuma a karshe, yana da muhimmanci a kiyaye hanyar da ta dace na tattaunawar da za ta kai ga zaman lafiya.

Hanyar da kasar Sin ke bi na samun zaman lafiya ta samo asali ne daga tsohuwar hikimar kasar Sin, kamar yadda yake bayyane a cikin wadannan kalamai: "Bai kamata masu karfi da masu kudi su rika zaluntar marasa karfi da matalauta ba", kuma "duk kasar da ke takama da karfin yaki, duk girmanta, daga karshe za ta durkushe." Wadannan kalmomi masu zurfi suna misalta kimar kasar Sin yayin da take tafiyar da tsarin kasa da kasa mai sarkakiya da rashin kwanciyar hankali, tare da neman hanyar zaman lafiya da ci gaba, ta hanyar tattaunawa da mutunta ’yancin juna ba tare da katsalandan ko shisshigi ba.

Abin da ke tattare da irin wannan yunkurin na kasar Sin shi ne wasu suka mayar da batun tattaunawa game da babbar hamayya tsakanin manyan tattalin arzikin duniya guda biyu. A wannan yanayi, an mayar da hankali kan Sin da Amurka a Gabas ta Tsakiya, da tabarbarewar alakar da ke tsakaninsu. Sanin kowa ne cewa Amurka da Isra'ila sun kulla alaka mai karfi ta tsaro, da tattalin arziki da siyasa. Kuma idan aka yi la'akari da yanayin siyasa mai sarkakiya a yankin, yin nazari game da dangantakar abota tsakanin kasar Sin da Falasdinu, wani zai dauka kasar Sin na kalubalantar Amurka ne. 

Kasar Sin ba ta da sha'awar kalubalantar Amurka a Gabas ta Tsakiya ko kuma a ko'ina. Tasirin da Amurka ke da shi a yankin na kara raguwa saboda tsarin siyasarta da bukatunta. Babu wanda za a zarga da sanyaya dangantakar Amurka da yankin Gabas ta Tsakiya face zabin da Amurka ta yiwa kanta.

Akidar Confucius ta kayyade cewa "ya kamata mutum ya nemi jituwa a cikin bambance-bambance kuma kada ya yi wa wasu abin da ba zai so a masa ba.” Burin kasar Sin shi ne ta samar da daidaito a wannan duniyar da ke cike da bambance-bambance. Kuma tana taimaka wa kasashen Gabas ta Tsakiya da hakan. (Yahaya Babs)