logo

HAUSA

Zuo Yu: Kasar Sin na kara samun sabbin abokai, kuma huldar dake tsakaninta da tsoffin abokai na karuwa

2023-06-19 19:48:14 CMG Hausa

Zuo Yu, ‘yar kasar Turkmenistan ce, wacce a halin yanzu take karatun digiri na biyu a fannin koyar da Sinanci a jami'ar Huaqiao dake Xiamen dake kudu maso gabashin kasar Sin, ta shafe shekaru 8 tana kasar Sin.

“Sinanci yana da ban sha'awa a gare ni, saboda yana daya daga cikin tsoffin harsuna da suka fi samu yawan masu amfani da shi a duniya. Ina shirin yin karatu a kasashen waje bayan na kammala karatun sakandare, a lokacin kuma na ga yarjejeniyar ilimi tsakanin ma’aikatar ilimi ta kasarmu da ta kasar Sin a yanar gizo, wato takardar da ke nuna cewa, ana iya neman izinin yin karatu a kasar Sin, kuma nan take na nema. Sannan na samu tallafin karatu na gwamnatin kasar Sin, don yin karatu a kasar a matsayin lamba daya a kasarmu.”

A shekarar 2015, Zuo Yu ta zo jami'ar horar da malaman koyarwa ta Nanjing domin koyon Sinanci, ta kuma ci jarrabawar kwarewar Sinanci a mataki na 5 a cikin shekara guda kacal, sannan ta koma jami'ar horar da malaman koyarwa ta Zhejiang don karantar wasan kwaikwayo, fina-finai da adabi. Bayan shekaru biyar da wani abu tana karatu da rayuwa a nan, ta kamu da son kasar Sin sosai, don haka ta yanke shawarar ci gaba da zama a kasar domin kara karatu. A shekarar 2021, ta zo jami'ar Huaqiao ta Xiamen don yin karatun neman digiri na biyu a fannin koyar da Sinanci ga masu magana da wasu harsuna. Yadda take rayuwa a kasar Sin a tsawon shekaru da yawa ya sa ta kara fahimtar harshen Sinanci.

“Harshe, a matsayinsa na mai daukar al'adu, yana nuna al'adun kasa kuma ya zama muhimmiyar hanyar sadarwa tsakanin kabilu daban-daban. Koyan Sinanci ya ba ni ra'ayoyi daban-daban, na yin tunani game da wasu batutuwa, harshen mahaifiyata da kuma harsunan waje da na kan koya, duka yaruka ne masu amfani da haruffa wajen harhada sauki da jera jimloli. Amma shi Sinanci yana amfani ne da alamomin akida, wanda ya bambanta da yaren da na sani. Sa'an nan, Sinanci harshe ne mai sauti, kuma kowace kalma tana da sauti, sautuna daban-daban na iya canza ma'anar kalma, yayin da ake magana da Sinanci, kamar rera waka ke nan.”

Ko da yake shekaru biyu kacal ke nan da zuwan ta Xiamen, amma Zuo Yu ta dade tana son wannan kyakkyawan birni mai bude kofa dake bakin teku. Ta ce Xiamen ya kasance tashar jiragen ruwa ta kasuwanci kuma kofa ce ta bude kofa ga kasashen waje, kuma a yanzu ta kasance yanki na musamman na tattalin arziki da birnin dake bakin teku mai budewa ake girmamawa sosai. Ta hanyar jirgin kasa ta musamman na Sin da Turai, ana iya zuwan Turai, Asiya ta Tsakiya, da Rasha kai tsaye daga Xiamen, kana ta hanyar tashar jiragen ruwa, ana iya hada kan birnin da kudu maso gabashin Asiya, Indiya, da kuma Japan.

“Ina jin dadin yin yawo a wannan birni, ina fuskantar teku, ina karanta littattafan da nake so. A gaskiya, na taba zuwa nan kafin in fara karatu a Xiamen, kuma tun daga lokacin na kamu da sonsa. Sararin sama mai shudi, ruwan teku mai tsafta, iska mai sanyi, da kamshin furanni, duk suna sa mutane su ji dadi da farin ciki. A cikin shekaru biyu da suka gabata, na kara fahimtar Xiamen. A matsayinta na cibiyar kasa, da ta ruwa da ke hade ‘Hanyar siliki ta kasa’ da ‘Hanyar siliki ta teku’, a bisa ga shawarar ‘Ziri daya da hanya daya’, Xiamen yana da tarihi a fannin kasuwanci da yin musaya tsakanin kasa da kasa. Akwai gine-gine iri-iri, da abinci mai dadi a nan, kuma ana iya gano alamomin hadin kan al'adun kasar Sin, da na kasashen waje, a zaman rayuwar yau da kullum na mazauna wurin.”

A cikin shekaru 8 da suka gabata da ta zaune a kasar Sin, darussan al'adu da ayyukan zamantakewa sun baiwa Zuo Yu damar zurfafa sanin dogon tarihi da kyawawan al'adun kasar Sin. Sinawa a ko da yaushe suna nacewa ga akida, da ra’ayin "neman fahimtar juna tare da kiyaye bambance-bambance", da "kimar daidaito", wanda kuma sun burge ta sosai. Ta ce, kasar Sin tana sa himma wajen yin mu'amala, da koyi da juna, tare da sauran al’ummomin duniya, kuma ra'ayinta da ya shafi zaman lafiya, ya zama wata dabi'a ta kasar ta son zaman lafiya a tsakanin jama'ar kasar Sin.

“Kasar Sin babbar kasa ce da ta kunshi kabilu 56 masu al'adu, harsuna da al'adu daban-daban. Akwai wasu bambance-bambancen al'adu tsakanin kudu da arewa, yamma da gabashin kasar Sin. Amma Sinawa na iya yin aiki tare da mutunta juna, da fahimtar juna domin ci gaban kasarsu. A cikin harabar makarantarnu, wadannan dalibai Sinawa masu al'adu daban-daban suna rayuwa tare cikin jituwa, kuma suna kasancewa tare da mu daliban kasashen waje, wadanda ke zuwa karatu a kasar ta Sin yadda ya kamata. Ko da yake ni da abokan karatuna na kasar Sin, muna da wasu bambance-bambancen da suka shafi cin abinci da zaman rayuwa, amma wadannan abubuwa ba sa kawo mana tsaiko wajen fahimtar juna ko zama abokai.”

A ra'ayin Zuo Yu, diflomasiyyar kasar Sin tana cike da kyautatuwa da kuma fatan alheri, don haka kasar Sin tana da sabbin abokai, kuma dangantakar dake tsakaninta da tsofaffin kawaye na kara karuwa.

A farkon wannan shekara, kasashen Sin da Turkmenistan sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, kan aikin gina "Ziri daya da hanya daya" tare. Zuo Yu ta ce, ko shakka babu kasashen biyu za su kara samun ci gaba sosai a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da hadin gwiwar makamashi, da ababen more rayuwa da dai sauransu.

“Shawarar ‘Ziri daya da hanya daya’ da kasar Sin ta gabatar, ta zo daidai da shawarar Turkmenistan ta farfado da tsohuwar hanyar siliki ta fuskar abubuwan dake cikinta. Kasar Sin tana da gogewa sosai a fannin gina ababen more rayuwa. Bayan da muka shiga wannan shawarar, kasarmu za ta samu karin jarin kayayyakin more rayuwa, kuma hakan zai kyautata yanayin zaman rayuwarmu.

Ban da wannan kuma, kasar Turkmenistan tana da albarkatun iskar gas mai yawa, kuma kasar Sin, a matsayinta na kasar da ta fi amfani da yawan makamashi a duniya, tana da matukar bukatar iskar gas. Bayan shiga shawarar 'Ziri daya da hanya daya', za a kara zurfafa hadin gwiwa a fannin makamashi a tsakanin kasashen biyu, wanda zai taimaka wajen tabbatar da tsaron makamashin Turkmenistan, da kuma inganta tsarin makamashinta.”

Da take magana kan makomarta, Zuo Yu ta ce, za ta ci gaba da zama a kasar Sin, don ba da gudummawa, wajen inganta cudanyar al'adu tsakanin Sin da kasashen tsakiyar Asiya.