logo

HAUSA

Kila kiwon kare a gida zai kare jarirai da kananan yara kamuwa da cutar fata nau'in eczema

2023-06-19 14:42:24 CMG Hausa

 

Wasu kan ce, kare, abokin arziki ne na dan Adam. Masu nazari na kasar Amurka sun ce, watakila kiwon kare a gida zai kare jarirai da kananan yara daga kamuwa da cutar fata nau'in eczema, cutar da ta sanya fata sauyawa zuwa launin ja ta rika kaikayi da kaushi.

Masu nazari daga kungiyar kiwon lafiya mai zaman kanta ta kasar Amurka wato tsarin kiwon lafiya na Henry Ford, ko kuma Henry Ford Health System a Turance sun gayyaci masu juna biyu dari 7 da 89 daga watan Satumban shekarar 2003 zuwa watan Disamban shekarar 2007, su shiga nazarinsu, inda masu nazarin suka rubuta yadda suka kiwata dabbobi a gida yayin da suke samun ciki da kuma shekara guda bayan haihuwa.

Yayin da masu nazarin suka bibiyi wadannan masu aikin sa kai, sun raba ‘ya’yansu zuwa rukunoni guda 4, wato wadanda ba su taba kamuwa da cutar fata nau'in eczema ba, da wadanda suka kamu da cutar yayin da shekarunsu suka kai 2 a duniya, amma sun warke yayin da shekarunsu suka kai 10, da wadanda suka yi ta fama da cutar yayin da shekarunsu suka kai 2 har zuwa 10, da kuma wadanda suka kamu da cutar yayin da shekarunsu suka wuce 10.

Masu nazarin sun gano cewa, masu juna biyu da yawansu ya kai kaso 26 cikin dari suna kiwon kare a gida. Wadanda suka kiwo kare a gida yayin da suke da ciki da kuma shekara guda bayan haihuwa, ‘ya’yansu da suka kamu da cutar fata nau'in eczema yayin da shekarunsu suka kai 2 a duniya, ba su da yawa. Duk da haka, kiwon kare a gida, ba shi da amfani sam ga wadanda suka haura shekaru 10 da kuma wadanda suka dade suna fama da cutar.

Madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin haske da cewa, sakamakon nazarin ya nuna mana cewa, shekara guda bayan haihuwa, muhimmin lokaci ne na yin rigakafin kamuwa da cutar fata nau'in eczema.

Masu nazarin suna ganin cewa, kiwon kare a gida a lokacin samun ciki da kuma shekara guda bayan haihuwa, yana kare jarirai da kananan yara daga kamuwa da cutar fata nau'in eczema. Kiwon dabbobi a gida yana ba da tasiri kan kwayoyin halittu da ke cikin hanjin jarirai da kananan yara.

Duk da haka masu nazarin sun nuna cewa, ba su tabbatar da cewa, kiwon kare a gida, dalili ne na kai tsaye da ya sa ake samun raguwar yawan jarirai da kananan yara wadanda suka kamu da cutar fata nau'in eczema ba. (Tasallah Yuan)