logo

HAUSA

"Kaunar Messi" Ya Nunawa Duniya Ainihin Kyawun Kasar Sin

2023-06-18 20:31:24 CMG Hausa

Idan aka waiwayi ziyarar da kungiyar kwallon kafa ta maza ta Argentina ta yi a birnin Beijing na kwanaki biyar, wani abin da ya fi daukar hankalin jama'a shi ne wasan sada zumunta tsakanin 'yan wasan kwallon kafa na maza na Argentina da na Ostiraliya a filin wasan ma’aikata wato workers stadium da yammacin ranar 15 ga wata. Kafofin yada labarai da dama na kasashen waje sun lura cewa da yawa daga cikin masoya kwallon kafa Sinawa da suka halarci wasan suna sanye da rigar kungiyar Argentina mai lamba 10 suna ta ihun sunan Messi. Kamar yadda Messi ya ce, “Ina jin a jikina irin kaunar da masoya ke dauke da shi da na zo kasar Sin a wannan karon.”

Hakan ya nuna wa duniya irin kaunar da jama'ar kasar Sin suke da shi ga wasan kwallon kafa da wasanni, tare da sakin jiki da mutane, da sha'awarsu, da sada zumunci. Wannan kuma ya haifar da ƙarin haske gami da irin bakin fenti da kafofin watsa labarai na yammacin duniya suke shafawa kasar Sin.

An yi matukar marhabin da ziyarar da Messi ya kai Sin, inda ya zama wata kafar fahimtar juna tsakanin Sin da sauran sassan duniya. Yaya kasar Sin take? Gani ya kori ji. Muna marhabin da abokai daga ko'ina a fadin duniya su zo su gane ma idanun su yadda hakikanin kasar Sin take. (Yahaya)