logo

HAUSA

Akwai kyakkyawar makoma game da hadin gwiwar Afirka da Sin a kokarin tinkarar kwararar hamada

2023-06-17 18:00:44 CMG Hausa

Yayin da ranar tinkarar kwararowar hamada da fari ke karatowa, an kaddamar da taron dandalin hamadar Taklimakan karo na 3, da kuma kwas din horar da fasahohin gina “babbar ganuwar” kare habakar hamada a Afirka karo na 2 a kwanakin baya, a garin Korla na jihar Xinjiang ta kasar Sin. A cikin wannan shiri za mu mai da hankali kan bukukuwan, gami da duba yadda ake gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin, ta fuskar tinkarar kwararowar hamada.