logo

HAUSA

Shin Ko Ziyarar Blinken A Kasar Sin Za Ta Bude Sabon Babin Kyautata Alakar Sin Da Amurka?

2023-06-15 15:41:20 CMG Hausa

A baya bayan nan an sanar da shirin sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken na gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin, ziyarar da za ta kasance mai matukar jan hankali, duba da yadda alakar Sin da Amurka ke cikin wani mawuyacin hali a halin yanzu.

Yayin zantawar da ministan harkokin wajen Sin Qin Gang ya yi da Blinken a jiya Laraba, Qin ya sake jaddada matsayar kasar Sin game da yankin Taiwan, yana mai jaddada dadaddiyar aniyar kasar Sin ta kare ikon yankuna, da mulkin dukkanin sassan kasar.

Kafin hakan, Amurka ta sha aiwatar da matakan tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, da suka hada da batun Taiwan, da yankin musamman na Hong Kong da batun jihar Xinjiang da dai sauran su.

Don haka masharhanta ke ganin ziyarar aiki da Blinken zai gudanar a Sin a ranaikun Lahadi da Litinin mai zuwa, za ta ba da zarafin tattaunawa kai tsaye tsakanin bangaren Sin da na Amurka, a irin yanayi da ba kasafai ake samun sa ba.

Tabbas hakan wata dama ce ta tattaunawa, tare da warware sabani kan muhimman batutuwan dake janyo hankulan sassan biyu, musamman a wannan gaba da kasashen biyu ke fatan farfado da nagartar alakarsu.

A bangaren kasar Sin dai a bayyane take cewa, babu abun da kasar ke fatan cimmawa illa bunkasa dangantaka da Amurka bisa tsarin mutunta juna, da wanzar da zaman lafiya da lumana, da cimma moriyar bai daya. Sai dai a bangaren Amurka, yanayin da ake gani daga manyan jami’an ta, da ’yan siyasar kasar na furta kalamai da fatar baki, da aiwatar da sabanin hakan, ya zamo babban dalilin dake mayar da hannun agogo baya, a kokarin da ake yi na dinke barakar kasashen biyu.

Yanzu dai abun jira a gani shi ne, ko ziyarar da Blinken zai gudanar ta wannan karo za ta share fagen warware sabani, da dora alakar sassan biyu kan turba ta gari. Ta yadda Amurka za ta amince da dakatar da tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin, da kaucewa yunkurin dakile ci gaban kasar ta hanyar sanya takunkumai marasa ma’ana, bisa fakewa da batun tsaron kasa ko wata takara maras adalci. (Saminu Hassan)