logo

HAUSA

Noma tushen Arziki

2023-06-14 08:38:30 CMG Hausa

Sanin kowa ne cewa a duk tsawon tarihin bil adama, fannin noma na cikin muhimman ayyuka da dan Adam ya fi baiwa fifiko, kasancewarsa bangare da ba za a iya rayuwa babu shi ba. Hasali ma dai noma shi ne kashin bayan rayuwar dan Adam, domin dai “Sai da ruwan ciki a ke jan na rijiya”.

La’akari da hakan ne ma ya sanya a nan kasar Sin, mahukunta ke kara azamar bunkasa fannin na noma a dukkanin bangarori, ta yadda a shekarun baya bayan nan, kasar ke ta kara samun karsashi da ci gaba a yawan yabanyar da ake samu. Ta amfani da na’urorin zamani, da fasahohi masu inganci, kasar Sin tana ta kara yawan mizanin hatsin da take nomawa a duk shekara, yayin da a hannu guda, manoman kasar ke ta samun karin kudaden shiga daga sana’arsu.

Bisa hakan, ma iya cewa Sin ta yi nasarar bunkasa yawan hatsi da take samu a duk shekara, ta kuma cimma nasarar samar da isasshen abinci ga miliyoyin al’ummar ta, kana sana’ar noma ta zamo wata dama ta fitar da dumbin al’ummar Sinawa daga kangin talauci.

A irin wannan lokaci duk shekara, wato tsakanin watannin Mayu zuwa karshen Yuni, manoman Sin na dukufa wajen girbin Alkama, wadda ke cikin abinci da ake da matukar bukatarsa a kasar.

Wasu alkaluma da aka fitar a baya bayan nan, sun nuna yadda adadin Alkamar da aka girbe a wannan lokaci ta haura mizanin Mu miliyan 239, wato kwatankwacin hekta miliyan 15.93. 

Kamar dai yadda ake yiwa noma kirari da “Na duke tsohon ciniki”, ma iya cewa a nan kasar Sin, sana’a ce wadda ta fitar da kasar kunya, domin ta haifarwa al’ummun ta tarin alherai a fannoni daban daban. Sai dai kuma a wani bangaren, sana’ar noma a kasar Sin ta samu tagomashi ne bayan da gwamnatoci a dukkanin matakai, suka yi aiki tukuru wajen samar da kyakkyawan yanayi na ci gaban sa, kamar fannin samar da rancen sayen na’urorin da manoma ke bukata domin aiki, da kudaden rance na sayen amfanin gona, da horas da malaman gona da manoma, da nazarin sabbin nau’oin iri da dai sauran su. (Saminu Hassan, Mohammed Yahaya, Sanusi Chen)