logo

HAUSA

Wanda Bai Ji Gari Ba…

2023-06-14 16:32:41 CMG Hausa

Yanzu haka hankalin duniya ya karkata kan matakin kasar Japan na zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku, duk da kashedin da masana da sassan kasa da kasa ke yi mata game da illar yin hakan ga duniya baki daya.

Tun lokacin da Japan ta bijiro da wannan aniya a shekarar 2021, bayan da wata girgizar kasar ranar 11 ga watan Maris din shekarar 2011 da ta lalata tashar nukiliyar Fukushima, tare da haddasa yoyon sinadarin nukiliya, aka rika nusar da Japan da ma wadanda suka bayar da shawarar aikata wannan danyen aiki.

Idan ba a manta ba, shi ma taron kasashen nan 7 masu karfin tattalin arziki a duniya wato G7 da ya gudana a kasar ta Japan, bai goyi bayan shirin kasar na zubar da ruwan dagwalon a cikin teku ba, saboda illarsa ga yanayin teku da tsaron abinci da ma lafiyar daukacin bil-Adama, amma bangaren Japan ya ci gaba da yin kememe da yin kunnen uwar shegu da neman kare kansa ta kowace hanya, wai don saboda arahar wannan tsari, wanda masu iya magana ke cewa, ba ta ado.

Idan har Japan ta damu da lafiya da tsaron al’ummarta da ma duniya baki daya, to ya kamata ta fahimci cewa, zubar da ruwan dagwallon nukuliya a cikin teku, batu ne da ya shafi duniya baki daya, saboda hadarin da ke tattara shi. Wannan ne ma ya sa a kwanakin baya wata tawagar masanan hukumar kula da makamashin nukuliya ta duniya IAEA ta ziyarci Japan, don gudanar da bincike bisa gaskiya da adalaci, da nufin fahimtar da mahukuntan kasar game da rashin fa’idar shirin ga rayuwar daukacin bil-Adama.

Don haka ya dace Japan ta bude ido da kunnuwanta ta kuma saurari abin da duniya ke fada game da illar da abin take son aiwatarwa. Idan kuma ta ki ji, to, ba za ta ki gani ba. Domin wanda bai ji gari ba, to kuwa zai ji Hoho. (Ibrahim Yaya)