logo

HAUSA

Me Ya Sa Aka Yi Maraba Da Messi Da Hannu Bibbiyu A Kasar Sin?

2023-06-14 15:32:23 CMG Hausa

Kwanan baya, labarin zuwan sarkin wasan kwallon kafa dan Argentina Lionel Messi kasar Sin, ya yi ta yawo a kafofin sada zumunta na kasar Sin. Masu sha’awar wasan kwallon kafa na kasar Sin sun yi maraba da shi da abokansa na kungiyar Argentina da hannu bibbiyu a ko ina. Tun tuni an sayar da dukkan tikitocin kallon gasar da za a yi tsakanin kungiyar Argentina da ta Australiya a ranar 15 ga wata.

Me ya sa aka yi maraba da Messi da hannu bibbiyu a kasar Sin? Saboda akwai dankon zumunci a tsakanin Sin da Argentina, al’ummun kasashen 2 suna mayar da juna abokai. Kafin shekarar 1972 da kasashen 2 suka kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu, an yi mu’amalar al’adu tsakanin jama’arsu.

Bayan kasashen 2 sun kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu kuma, a matsayinsu na manyan kasashe masu tasowa a duniya, suna mara wa juna baya a fannonin kiyaye ikon mulkin kasa da cikakkun yankunan kasa. Suna da buri iri daya a fannonin kara azama a fannin ci gaban tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama’a. Kasashen 2 suna ta inganta dangantakarsu.

Yin mu’amala tsakanin jama’a, wata kyakkyawar gada ce ta raya hulda tsakanin kasashen Sin da Argentina. A shekarun 1990, shahararren dan wasan kwallon kafar Argentina Diego Armando Maradona, ya ziyarci kasar Sin sau da dama. Messi ya gaji irin wannan al’ada ta hanyar kawo wa kasar Sin ziyara har sau 7.

Nan gaba ba da dadewa ba, a nan Beijing, masu sha’awar wasan kwallon kafa na kasar Sin za su ji dadin kallon wata gasa mai kayatarwa, inda za su kara fahimtar sha’awar wasan kwallon kafa, da kwarewar ‘yan wasan kwallon kafa na Argentina wadanda suka ci kofin duniya da ya gabata. Haka kuma, al’ummun Sin da Argentina za su kara sanin dankon zumuncin da ke tsakaninsu, duk kuwa da nisan da ke tsakanin kasashen 2. (Tasallah Yuan)