logo

HAUSA

Sin da Afirka na hadin gwiwa don neman ci gaba mai dorewa

2023-06-13 16:08:04 CMG Hausa

A kwanakin baya, an gudanar da taron muhallin rayuwar dan Adam karo na 2 a birnin Nairobi na kasar Kenya, inda aka mai da hankali kan batun neman ci gaban kasa mai dorewa. Na lura da yadda a wajen bikin kasar Sin ta gabatar da dabarunta a fannin raya birane da kauyukanta, wadanda suka janyo hankalin bangarori masu halartar taron. Musamman ma wani rahoton bincike da jami’ar Tongji ta kasar Sin ta gabatar, wanda ya bayyana matakan da kasar Sin ta dauka a wasu kauyukan dake bakin teku, inda ta wadannan matakai an samu damar wadatar da mazauna kauyukan, ba tare da fitar da karin hayaki mai dumama yanayi ba. Wasu jami’an hukumar kula da muhallin rayuwar dan Adam ta MDD sun yaba wa kasar Sin bisa wadannan matakan da ta dauka, inda suka ce aikin tamkar “bude wata sabuwar hanyar samun ci gaba ga duk duniya ce.”

A matsayina na wani Basine, na gane ma idanuna yadda ake ta samun nasarori a kasar Sin ta fuskar neman ci gaban kasa mai dorewa, musamman ma a shekarun baya: motoci masu yin amfani da wutar lantarki dake gudu a tituna suna ta karuwa, kana ana samun karin kwanakin da ake samun yanayi mai kyau wanda ya ba mutane damar shakar iska mai tsabta, yayin da ake ta kokarin gina wuraren shakatawa a cikin birane don kayatar da muhalli. Sa’an nan muhallin kauyuka na kara zama mai tsabta da kayatarwa, abun da ya janyo dimbin mutane masu yawon shakatawa.

Sai dai a sa’i daya, bisa matsayina na mai kaunar Afirka, ni ma ina son kasashen Africa su amfana da fasahohin kasar Sin na neman ci gaba mai dorewa, ta yadda a nahiyar Afirka ma ake iya samun ci gaba iri daya. Abun dake sa ni alfahari da farin ciki shi ne, wannan burin da na sanya ya cika.

Yanzu haka, ana iya ganin yadda kamfanonin kasar Sin ke yin amfani da fasahohinsu wajen taimakawa kokarin kasashen Afirka na samun ci gaban tattalin arziki mai dorewa, a duk wata kasar dake nahiyar Afirka.

Shin abokaina dake zama a birnin Abuja na Najeriya kun taba lura da wutan danja masu yin amfani da makamashin zafin rana, wadanda aka saka su a dab da titunan birnin? Gaba daya akwai su guda 719, wadanda ba su tsoron katsewar wutar lantarki, ganin yadda suke samun makamashi daga rana kai tsaye. Wadannan wutan danja sun zo ne daga kasar Sin.

Haka kuma, a watan Janairun bana, an kaddamar da wani sabon layin dogo a birnin Lagos, wanda wani kamfanin kasar Sin ya dauki nauyin gina shi. Ana yin amfani da wutar lantarki mai tsabta wajen gudanar da aikin zirga-zirgar jirgin kasa a kan wannan layi, kana an samu damar takaita lokacin zirga-zirga daga mintuna 90 zuwa wasu 20.

Haka zalika, a lokacin da ake gudanar da taron muhallin rayuwar dan Adam a wannan karo, wani kamfanin kasar Kenya ya samar da dimbin motocin bas na wutar lantarki, don masu halartar taron sun yi amfani da su. Sai dai fasahohin sarrafa wadannan motoci sun zo daga wani kamfanin kera motoci na kasar Sin.

Ban da wannan kuma, a kasar Zambia, an kaddamar da wata tashar wutar lantarki mai yin amfani da karfin ruwa, wadda wani kamfanin kasar Sin ya gina, a watan Maris na bana. Ta wannan hanya kasar ta samu karin karfin samar da wutar lantarki na Megawatt 750, wanda ya taimakawa daidaita matsalar karancin wutar lantarki a Lusaka, hedkwatar kasar Zambia.

Sa’an nan a Addis Ababa na kasar Habasha, wani kamfanin kasar Sin ya dauki nauyin kwaskwarimar, inda aka mai da shi wani ni’imtaccen wuri na yawon shakatawa. Wannan wurin nishadi ya samar wa mutane da damammakin shan iska, da gudanar da aikin ban ruwa, da zirga-zirgar motoci, ta yadda ya zama wani muhimmin wuri mai kayatarwar muhalli.

Ya kamata mu lura da cewa, kasar Sin ita ma ba ta samu damar raya kasa ta wata hanya mai dorewa cikin sauki ba. Kana Sinawa su ma sun taba damuwa sosai sakamakon matsalar gurbacewar iska, da kasa, gami da ruwa. Sai dai daga bisani, bisa samun jagoranci mai karfi, da tsara ingantattun manufofi masu dacewa, da tsayawa kan aiwatar da shirin da aka tsara, kasar ta samu ci gaba sosai, a fannonin dakile gurbacewar muhalli, da rage hayakin dake dumama yanayi, da kyautata muhallin rayuwar dan Adam, da dai makamantansu. Haka zalika kasar ta samu wata daidaitacciyar hanyar raya kasa, wadda ke biyan bukatun raya tattalin arziki, gami da na kyautata muhalli.

Yanzu haka, kasar Sin na son samar da fasahohin da take da su ga sauran kasashe masu tasowa, ta yadda za su iya magance yin kuskure, yayin da suke kokarin raya kai. Ban da haka, su kamfanonin kasar Sin su ma za su iya samun riba, ta hanyar mika fasahohi masu inganci na rage yawan hayakin dumama yanayi da na kare muhalli ga sauran kasashe.

Ta haka za mu iya ganin cewa, kasar Sin da kasashen Afirka suna gudanar da hadin gwiwa mai dorewa dake amfanar juna, don tabbatar da ci gaban tattalin arziki da zaman al’ummarsu mai dorewa. A kan wannan turba mai dacewa na hadin gwiwa da neman ci gaba, Sin da Afirka suna tafiya tare. (Bello Wang)