Ga yadda wata tawagar sojojin kasar Sin dake tabbatar da zaman lafiya a kasar Mali ta gina wasu dakunan karatu
2023-06-12 09:25:09 CMG Hausa
Ga yadda a kwanan baya, wata tawagar sojojin kasar Sin karo na 10 dake tabbatar da zaman lafiya a kasar Mali a madadin MDD, ta kebe kudi da lokaci, don taimakawa makarantun firamare biyu na wurin, wajen gina wasu dakunan karatu, har ma ta samar da wasu kayayyakin koyarwa, kamar su teburan karatu, da alluna, da kuma kantocin ajiye litattafai, domin kokarin kyautata yanayin karatu da zaman rayuwa da yaran wurin suke ciki. (Sanusi Chen)