logo

HAUSA

Tsarin jiki na lokacin yarantaka yana da nasaba da kwarewar fahimta a lokacin shiga matsakaitan shekaru na rayuwa

2023-06-12 15:37:46 CMG Hausa

 

Wani binciken da aka gudanar ta hanyar bibbiya a kasar Australiya ya nuna cewa, makin da kananan yara suka samu cikin jarrabawar tsarin jiki, yana da nasaba da kwarewarsu ta fahimta a lokacin da suka shiga matsakaitan shekaru na rayuwa. Kana irin wannan alaka ba ruwanta da kwarewarsu a fannin karatu a lokacin yarantaka, matsayinsu a zamantakewar al’ummar kasa, al’adarsu ta shan taba ko giya a lokacin shiga matsakaitan shekaru na rayuwa. Don haka mai yiwuwa ne za a dauki matakan yin rigakafin koma bayan kwarewar fahimta tun daga lokacin yarantaka.

Jami’ar Monash ta kasar Australiya ta kaddamar da wata sanarwa a kwannan baya, inda ta ce, masu nazarin sun tantance bayanan mutane fiye da dubu 1 da dari 2 wadanda aka dauki shekaru fiye da 30 ana bibiyarsu, a kokarin gano alakar da ke akwai tsakanin lafiyar kananan yara da tsarin jikinsu da kuma kwarewarsu ta fahimta a lokacin shiga matsakaitan shekaru na rayuwa.

A shekarar 1985, an gudanar da binciken kan kananan yara dubu 1 da dari 2 da 44 wadanda ke cikin shekaru 7 zuwa 15, inda aka binciko zukatansu, huhunsu, karfin jijiyoyinsu, juriyarsu da dai sauransu. Daga shekarar 2017 zuwa 2019 kuma, masu nazarin sun jarraba kwarewar fahimtar wadannan mutane ta hanyar amfani da kwamfuta, wadanda ke cikin shekaru 39 zuwa 50.

Sakamakon binciken ya nuna cewa, idan wasu suna da koshin lafiya a zuciya, huhu da jijiyoyi, kana ba su da kiba, a lokacin yarantaka, to, sun fi samun maki mai kyau ta fuskar daidaita bayanai cikin kwakwalwa, mai da hankali kan wani abu da cikakkiyar kwarewar fahimta a lokacin shiga matsakaitan shekaru na rayuwa. Kuma irin wannan alaka ba ruwanta da kwarewarsu a fannin karatu a lokacin yarantaka, matsayinsu a zamantakewar al’ummar kasa, al’adarsu ta shan taba ko giya a lokacin shiga matsakaitan shekaru na rayuwa.

Masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, mai yiwuwa a fara fama da matsalar raguwar kwarewar fahimta tun lokacin shiga matsakaitan shekaru na rayuwa, lamarin da watakila zai sa a kamu da cutar karancin basira da sauran cututtukan dake shafar kwakwalwa, har su shafi yanayin koyo da adana muhimman abubuwa a lokacin da mutane suka tsufa. Saboda haka akwai bukatar daukar matakan yin rigakafin koma bayan kwarewar fahimta tun daga lokacin yarantaka. (Tasallah Yuan)