Afirka ta yi matukar murna da zuwan gasar ITTF nahiyar
2023-06-15 19:11:40 CRI
Zuwan gasar kasa da kasa ta kwallon tebur nahiyar Afirka, abu ne da aka jima ana dakon sa, kuma faruwar hakan ta sanya al’ummar nahiyar nuna matukar farin ciki da annashuwa.
Yanzu haka dai an kammala gasar ta ITTF ta shekarar 2023, a birnin Durban na Afirka ta kudu, wanda hakan ya kasance karon farko da babbar gasar ta duniya ta sake gudana a Afirka a tsawon shekaru 84.
A wasan zangon farko an fafata tsakanin Ibrahima Diaw daga Senegal, da takwaransa na Afirka ta kudu Dean Levy, Ibrahima Diaw ya yi nasara, duk da cewa ‘yan wasan 2 sun taka rawar gani a gasar yadda ya kamata.
Da yake tsokaci game da hakan, Ibrahima Diaw wanda ke matsayi na 119 a duniya a kwallon tebur ya ce "Wannan ne karon farko da aka gudanar da gasar a bainal jama’a cikin tsawon lokaci. Na yi farin cikin wakiltar nahiyar Afirka a wannan gasa da ta gudana a nahiyar mu. Ni da sauran wakilan kasashen nahiyar za mu yi iya kokarin mu wajen daga darajar Afirka".
Shi ma a nasa bangaren, duk da ya rasa nasarar lashe lambar karramawa ta gasar, dan wasa Dean Levy mai shekaru 18 da haihuwa, ya ce zuwan sa gasar ya kara masa karsashi sosai. Ya ce "Ina alfahari sosai. Dama ce da ba kowa ke samun irin ta ba, wato halartar babbar gasa irin wannan. Kuma kasancewar kasar mu mai masaukin bakin gasar, wadda ta samu ‘yan kallo masu tarin yawa, abu ne da ban taba mafarkin faruwarsa ba”.
Kari kan hakan, dan wasan na Afirka ta kudu ya ce sun samu damar kallon manyan wasanni daga kwararrun ‘yan wasa, kuma ‘yan kallo sun samu zarafin shiga a dama da su a gasar ta wannan karo. An kafa teburan wasan a wajen zauren gudanar da gasar dake babban dakin taro na kasa da kasa dake Durban wato ICC, wanda hakan ya baiwa al’umma damar buga wasanni kanana tare da iyalai da abokan su.
Yayin gasar, an makala manyan kyallayen tallar kwallon tebur din a turakun fitulun haskaka tituna dake sassan birnin Durban, wanda hakan ke kara tunatar da jama’a game da gudanar babbar gasar ta ITTF. Da zarar mutum ya shiga birnin Durban, zai ci karo da rukunonin makada da mawakan gargajiya, inda kuma masu rawar ‘yar tsana na 'Takuma' ke cashewa, a babban filin jiragen sama na kasa da kasa na King Shaka.
Yayin bude gasar, shugaban hukumar ITTF Petra Sorling, ya ce gudanar da wannan gasa a Durban, ya wuce batun shagalin wasa kadai, domin kuwa hakan ya kara nuna kwazon ITTF, a fannin yayata wasan kwallon tebur zuwa nahiyoyi da al’adu daban daban.
Shi ma babban jagoran ITTF Steve Dainton, ya jaddada muhimmancin komawar gasar zuwa Afirka, bayan shekaru 84. Steve Dainton ya ce "Kwallon tebur babban wasa ne a duniya baki daya. Muna son ganin ya shiga sahun gaba a duniya, don haka ne yake da muhimmanci mu rika gudanar da wannan babbar gasa a dukkanin sassan duniya”.
Yadda gasar ta shekarar 2021 ta gudanar a birnin Houston na Amurka, da guda biyu na bayan ta da suka gudana a Asiya da turai, ya nuna aniyar hukumar ITTF na kokarin yada gasar zuwa dukkanin sassan duniya.
Dainton ya kara da cewa, "Fatan mu shi ne a shekarar 2027, mai yiwuwa mu iya zuwa Latin Amurka ko Oceania, saboda abu ne mai muhimmanci wannan wasa ya kasance na duniya baki daya”.
Yayin wasannin atisaye da hukumar gudanarwa ta kwallon tebur ta kasar Sin ko CTTA ta shirya, manya kocin wasan na kasar Sin Liu Zhiqiang da Li Dacheng, sun jagoranci baiwa kungiyar Afirka ta kudu horo, musamman a fannonin mika kwallo da karbar kwallo daga abokan wasa.
Game da hakan, dan wasan kungiyar Levy ya ce "Damar da muka samu ta samun horo daga tawagar kasar Sin muhimmiya ce, wadda ba mu samu irin ta ba a baya. Kocin kasar kwararre ne, yana da sani a fannonin wannan wasa da yawan gaske, ina ganin kwarewarsa za ta amfani mutane da dama, musamman kungiyoyin wasan na Afirka dake da bukatar kara kwarewa. A daya bangaren kuma, wannan gasa ta bude mana karin fannoni na wasan kwallon tebur da a baya ba mu sani ba, mun kuma hadu da kwararrun ‘yan wasa na duniya, ciki har da Ma Long, dan wasa mafi kwarewa a wasan. Hakan ya ba mu sha’awa matuka”.
Ko shakka ba bu gudanar da wannan muhimmiyar gasa a birnin Durban, ta karfafa gwiwar ‘yan wasan kwallon tebur dake nahiyar Afirka a nan gaba.
A nasa bangare, Ibrahima Diaw daga Senegal cewa ya yi, "Akwai tarin ‘yan wasa masu kwarewa a Afirka. Don haka ina fatan za mu samu karin kwararrun ‘yan wasa matasa a nan gaba".
Shi ma kwararren dan wasan kwallon tebur na Najeriya, wanda shi ne na 12 a duniya Quadri Aruna ya ce "Karbar bakuncin wannan babbar gasa ta duniya ba wai ta shafi Afirka ta kudu ba ne kadai, batu ne da ya shafi nahiyar Afirka baki daya. Yayin gasar ta wannan karo, na rika jin kamar ina wasa ne a gida". Quadri Aruna ya bayyana hakan ne bayan da ya lashe wasan da ya buga a zagayen gasar na farko.
Aruna ya kara da cewa, "Ko shakka ba bu, buri na shi ne na karfafa gwiwar matasan ‘yan wasan nahiyar mu ta Afirka".