Ministan wajen Zimbabwe: Zamanintar da Sin na yin tasiri mai yakini ga duniya
2023-06-10 16:04:08 CRI
A kwanakin baya ne ministan harkokin wajen kasar Zimbabwe Frederick Shava ya yi tsokaci cewa, salon zamanintarwa na kasar Sin yana kawo tasiri mai yakini ga duk duniya:
A zantawar Mista Shava da wakilin CGTN yayin da yake halartar taron dandalin tattaunawa kan harkokin kasuwanci tsakanin kasar Sin da Zimbabwe da aka shirya a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, ya karyata zargin da wasu kafofin watsa labarai na kasashen yamma suka yi, wai kasar Sin ta dana tarkon bashi ga kasashen Afirka ta hanyar zuba jari. Ya kara da cewa, kasarsa tana da arzikin albarkatu masu tarin yawa, amma tana karancin fasaha da kwararru, musamman ma a bangarorin ma’adinai da gine-gine da fasahar sadarwa da sana’ar yawon bude ido, don haka ya yi imanin cewa, bunkasuwar wadannan sassa na bukatar zuba jari da goyon bayan fasaha daga kasar Sin.
Kana Shava ya yaba da kokarin da kasar Sin take yi domin zamanintar da kasar, inda ya bayyana cewa, babban sakamakon da kasar Sin ta samu ya yi tasiri mai yakini ga sassan duniya baki daya.