logo

HAUSA

Yadda ake darajanta wayewar kan kasa da kasa

2023-06-13 21:44:31 CRI

 

Yau ina so mu kalli wani gajeren bidiyo game da al’adun bil Adama:

 

wayewar kan kasa da kasa ta kashe kwarkwatar idonmu, inda wayewar kan al’ummar Sinawa ta kasance a sahun gaba, wadda ake gada daga zuriya zuwa zuriya.

Tsoffin garuruwan da Sinawa suka gina shekaru 5000 da suka gabata, harufan Sinanci da aka sassaka a kan allunan kasusuwan dabbobi, kayayyakin tarihi masu daraja da aka adana sun bude mana kofar fahimtar tarihi.

A gabashin duniya, ko a yammanci, a Asiya, ko a Afirka, ana kokarin gadon al’adu masu dogon tarihi har zuwa wannan zamanin da muke ciki.

Duk da cewa, akwai bambanci tsakanin wayewar kai, amma babu wayewar kan da ta fi wata inganci, hikimomin bil Adama sun rage bambancin dake tsakanin sassan duniya, yadda ake gada da cudanyar al’adu za su taimaka wajen kara kyautata yanayin duniyarmu yadda ya kamata.