logo

HAUSA

Wuraren da aka gudanar da gasar Olympic ta birnin Beijing dake manyan makarantu sun kafa muhimmin tarihi

2023-05-25 08:00:00 CRI

Yayin wasannin gasar Olympic da aka gudanar a birnin Beijing a shekarar 2008, ‘yan wasan motsa jiki na Sin su 4, sun lashe lambobin zinari a wasannin judo da taekwondo, wasanni da suka gudana a filin wasannin motsa jiki dake jami’ar koyon ilimin kimiyya da fasaha dake birnin Beijing ko USTB a takaice. Shekaru 15 bayan hakan, ‘yan wasan da suka lashe lambobin na yabo sun koma wannan wurin wasannin motsa jiki dake jami’ar ta USTB, domin duba yanayin bayar da horo ga daliban jami’ar.

Cikin tsokacin da suka yi yayin zuwan su jami’ar, ‘yan wasan da suka lashe lambar zinari a wasan Judo Xian Dongmei, da Yang Xiuli, da Tong Wen, da dan wasan da ya lashe lambar zinari a wasan taekwondo Wu Jingyu, sun zama mambobin farko na jami’ar ta USTB, da suka shiga kundin bajimtar makarantar a watan da ya gabata. Baya ga ‘yan wasan 4, an kuma shigar da ‘yar wasan jifan mulmulallen karfe ajin mata Gong Lijiao, wadda ita ma ta kammala karatun ta a jami’ar, cikin jerin ‘yan wasa mafiya hazaka na makarantar, bayan da ta yi nasarar lashe lambar zinari a gasar Olympics ta birnin Tokyo a shekarar 2020.

Game da hakan, wani babban jami’in jami’ar ta USTB Sun Jinghong, ya ce baya ga fannin horas da kwararrun masana karafa da dangogin su, jami’ar su ta shahara, wajen dora muhimmancin gaske ga horas da dalibai a fannonin motsa jiki, inda jami’ar ke yayata ruhin wasannin Olympic ta hanyar gudanar da kwasa-kwasai daban daban, da ayyuka mabanbanta da suka shafi motsa jiki.

Shi ma babban manajan cibiyar gudanarwa ta wuraren da ake gudanar da wasanni a jami’ar Ju Yang, cewa ya yi an bude zauren wasannin tsalle-tsalle na jami’ar ne ga al’umma tun a watan Afirilun shekarar 2009. Kuma tun bayan hakan, wuraren suka zama alamar martabar jami’ar ta USTB.

A nata bangare kuwa, wata tsohuwar ‘yar wasan taekwondo Wang Linru, cewa ta yi, kafin ta shiga jami’ar ta USTB domin karatun digiri a shekarar 2016, wuraren wasannin Olympic dake jami’ar na cikin dalilan ta na zabar jami’ar.

Bayanai daga tsangayoyin koyon ilimin wasannin motsa jiki a jami’ar ta USTB, sun nuna cewa akwai kwasa-kwasai 21 karkashin sassa 50 da dalibai ke iya shiga, yayin da kungoyoyin wasanni na dalibai guda 26, ke shirya sama da wasanni 70 a duk shekara, karkashin jagorancin babbar tsangayar wasannin makarantar.

Shi kuwa mataimakin farfesa a jami’ar ta USTB, wanda ke koyarwa a sashen tattalin arziki da gudanarwa Liu Mingzhu, cewa ya yi jami’ar su tana karfafa gwiwar dalibai da su kara shiga harkokin wasannin motsa jiki, wanda a cewar sa fanni ne da ake gudanar da shi duk tsawon rayuwa.

A daya bangaren, wani dalibin jami’ar da ya kware a wasannin volleyball, da badminton da kwallon tebur mai suna Freshman Huang Zhouyang, cewa ya yi, ya yi sa’ar kasancewa dalibi a jami’ar USTB, domin kuwa ya samu damar koyon ilimi, da motsa jiki, da koyon dabi’un wasannin Olympic.

Bugu da kari, wani malami dake koyarwa a sashen wasannin motsa jiki na jami’ar ta USTB mai suna He Qun, cewa ya yi wuraren wasannin Olympic dake jami’ar sun taimaka wajen baiwa sashen sa damar gudanar da horo ga ‘yan wasan sauran sassan jami’ar a mataki na kwarewa. He ya ce "Da yawa daga mambobin sassan jami’ar mu sun zama kwararru a fannonin wasannin motsa jiki a matakin kasa, ciki har da wasannin judo, da taekwondo, da kwallon tebur, da ninkaya da kwallon kwando".

A bangaren sa kuwa, mamba a hukumar kare al’adu da abubuwan da aka gada daga gasar Olympic, karkashin kwamitin shirya gasar Olympic ta kasa da kasa Hou Kun, cewa ya yi wuraren wasannin Olympic dake cikin jami’o’i a yanzu sun zama wuraren gudanar da wasannin motsa jiki, da samar da horo ga ‘yan wasa da kuma sauran al’umma dake son motsa jiki, inda suka kasance kyakkyawan misali na yadda ya dace a dore da amfani da wuraren.

Wata dalibar ta daban da ita ma ta fara karatu a jami’ar tun a shekarar 2007 mai suna Gong Lijiao, ta ce ta yi farin ciki da ganin dorewar wasanni, da yadda suka zama wani bangare na rayuwar daliban jami’ar. Gong Lijiao ta ce "Motsa jiki ya zama wata al’ada a jami’ar mu, kuma mai yiwuwa sanya wadanda suka yi kwazo a kundin ‘yan wasan jami’ar mafiya hazaka, zai ingiza karin matasa zuwa ga kokarin cimma nasarar mafarkin su".