An yi kira da a kiyaye tsarin hana yaduwar makaman nukiliya da dokokin kasa da kasa
2023-06-09 21:42:14 CMG Hausa
A yayin taron hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA) da aka gudanar a cikin watan Yuni, mahalarta taron sun nuna adawa da hadin gwiwa tsakanin kasashen Amurka da Birtaniya da Australia kan jirgin yakin karkashin teku mai amfani da makamashin nukiliya. Wakilin kasar Sin ya gabatar da jawabi na musamman kan wannan batu, inda ya yi kira ga dukkan bangarorin da su hada kai wajen inganta tsarin tattaunawa tsakanin gwamnatoci. Wakilai daga kasashe sama da 20 da suka hada da Rasha, da Pakistan, da Indonesiya, da Brazil da sauransu, sun yi na'am da matsayi da ma shawarar kasar Sin, tare da yin kira da murya daya na kiyaye tsarin hana yaduwar makaman nukiliya na kasa da kasa da ma dokokin kasa da kasa.
Wannan shi ne karo na takwas a jere da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ke yin la'akari da wannan batu, ta hanyar tattaunawa tsakanin gwamnatocin kasashen duniya, lamarin da ya sake dakile yunkurin kasashen Amurka da Birtaniya da Australia na tilastawa sakatariyar hukumar. Wannan hadin gwiwa na "AUKUS" tana amfani ne kawai da hadin gwiwar karkashin ruwa ta nukiliya a matsayin hujja don amfani da kasar Australia a matsayin hanyar ciyar da dabarun siyasar Amurka gaba, da kwaikwayon dabarun NATO na haifar da rikice-rikice na yanki da kuma tunkarar yankin Asiya da Pacific, don biyan bukatu na kashin kai. (Ibrahim)