logo

HAUSA

Tafiya Da Gwani Mai Dadi

2023-06-08 20:28:42 CMG HAUSA

DAGA SAMINU ALHASSAN

Yayin da kasashen Afirka ke kara nuna amincewa da kasar Sin a fannonin hadin gwiwar wanzar da ci gabansu, karin kasashen nahiyar na dada zurfafa hadin gwiwa, da bunkasa ci gaban alakar dake tsakaninsu yadda ya kamata.

Hakan ne ma ya sa a baya bayan nan shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, yayin da yake karbar takardar kama aiki daga sabon jakadan Sin a kasar sa Zhou Ding, ya jaddada burinsa na fadada hadin kai da bangaren kasar Sin a fannoni daban daban.

Ga duk mai bibbiyar yanayin alakar dake tsakanin Sin da Zimbabwe, ya kwana da sanin yadda Sin din ta jima tana tallafawa Zimbabwe wajen samar da ababen more rayuwa, ta hanyar samar da kudaden gudanar da manyan ayyukan raya kasa, ciki har da katafaren ginin ofishin majalissar dokokin kasar, da fadada tashar samar da lantarki ta tururi mai zafi, da sake fasali, da kuma fadada babban filin jiragen sama na Robert Mugabe, da zango na uku na aikin samar da hidimar wayar salula ga al’ummar kasar, ayyukan da suka yi matukar taka rawar gani a fannin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Zimbabwe.

Bahaushe kan ce “Tafiya da gwani mai dadi”. A gani na hakan ne ma ya sanya kasashe masu tasowa ke dada fifita alakar su da Sin, idan ana batun alakar kasa da kasa, kasancewar kasar Sin na nacewa manufar kaucewa tsoma baki cikin harkokin wajen sauran kasashe, da nuna adawa da takunkuman da kasashen yamma ke kakabawa sauran kasashe, ciki har da irin wadanda aka kakabawa kasar ta Zimbabwe. Baya ga haka, kasar Sin ta yi cudanya, tare da mara baya ga kasashen Afirka, a fannin samar da tallafin yaki da annobar COVID-19 wadda a ’yan shekarun da suka gabata ta addabi duniya baki daya.

Hakan ne ma ya sa masharhanta da yawa ke hasashen kara kyautatuwa, da yaukaka, da dorewar alakar Sin da abokan tafiyarta wato kasashe masu tasowa, wadanda suka amince su yi tafiya kafada da kafada da Sin din bisa mutunta juna, da zurfafa musaya a fannonin hadin gwiwa daban daban, karkashin manufofi irin na “Shawarar ziri daya da hanya daya”, da manufar bunkasa ci gaban duniya baki daya.