OECD ta daga hasashen bunkasar tattalin arzikin duniya na bana zuwa 2.7%
2023-06-08 10:41:42 CMG Hausa
Kungiyar kasa da kasa ta bunkasa hadin gwiwar raya tattalin arziki da ci gaba ko OECD, ta dan daga matsayin hasashenta game da mizanin bunkasar tattalin arzikin duniya na bana ko GDP zuwa kaso 2.7 bisa dari.
Kungiyar wadda ta bayyana hakan a jiya Laraba cikin wani rahoto da ta fitar, ta ce hauhawar farashin kayayyaki ya dan ragu, kuma kara bude kofofi da kasar Sin ta yi, ya zaburar da bunkasar tattalin arzikin duniya. To sai dai kuma ta yi gargadin cewa, “sai an kai ruwa rana” kafin tattalin arzikin duniyar ya farfado yadda ya kamata.
Bisa hasashen kungiyar, kasar Sin za ta samu saurin bunkasar tattalin arziki tsakanin shekarar 2022 da 2023, sama da na dukkanin kasashe mambobin kungiyar G20, musamman sakamakon dage tsauraran matakan yaki da annobar COVID-19 da kasar ta aiwatar. Sabo da haka, ana hasashen bunkasar GDPn kasar ta Sin zai daga zuwa kaso 5.4 a shekarar nan ta 2023. (Saminu Alhassan)