logo

HAUSA

Dalilin da ya sa yankin Latin Amurka ke son fadada hadin gwiwa da kasar Sin

2023-06-07 09:52:56 CMG Hausa

Ana karancin furannin Rose na kasar Ecuador a birnin Guangzhou na kasar Sin, kasar Cuba da sauransu, sun bude kantuna a dandalin cinikayya na yanar gizo na kasar Sin, haka kuma ana samun karuwar naman sa na yankin a kasuwar kasar Sin. Me ya sa ake samun kyautatuwar alaka tsakanin Sin da Latin Amurka?

Watakila za a iya samun amsar a hirar da aka yi da Ernesto Samper, tsohon shugaban Columbia a kwanan nan, inda yake cewa: “muna bangaren Fasifik, kuma muna fatan za a samu wani shirin bai daya na raya fadin yankin Fasifik.” Wannan shiri na bai daya na nufin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da kasar Sin ta gabatar.

Babban burin raya shawarar Ziri Daya da Hanya Daya shi ne, kara yawan cinikayya tsakanin Sin da Latin Amurka, ta yadda Latin Amurka za ta ci gajiya daga ci gaban kasar Sin. A yanzu haka, kasar Sin ce kasa ta biyu mafi yawan cinikayya da Latin Amurka cikin shekaru 10 a jere. A shekarar 2022, yawan cinikayya tsakanin bangarorin biyu ya kai dala biliyan 485.79, wanda ya kasance wani sabon adadin da ya kai matsayin koli. Baya ga haka, wasu ayyukan dake karkashin shawarar, sun inganta ci gaba da samar da ayyukan yi kai tsaye, a yankunan karkarar kasashen Latin Amurka, kuma sun kyautata rayuwar jama’a. Abu mafi muhimmanci shi ne, shawarar ta ingiza wani sabon kuzari ga ci gaban kasashen Latin Amurka tare da bunkasa karfinsu na samun ci gaba da kansu. Yanzu, sabbin ababen more rayuwa da ake ginawa sun zama wani sabon abun dake haskaka hadin gwiwar Sin da Latin Amurka.

Mutane da dama daga Latin Amurka sun yi ammana cewa, shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, ba abu ne na tilas ba, kuma ba ta da alaka da sharudda na siyasa, sai dai ma sabbin dabaru da sabuwar hanyar ci gaba da take gabatarwa. A bana shawarar Ziri Daya da Hanya Daya ke cika shekaru 10. Kuma Kasar Sin na neman zamanantar da kanta ta hanyar ci gaba mai matukar inganci da zai samar da karin damammaki ga kasashen dake fadin duniya, cikinsu har da kasashen Latin Amurka.(Fa’iza Mustapha)