Yadda za a kiyaye da zamanantar da al’adu
2023-06-07 08:34:01 CMG Hausa
Al’ada wata muhimmiyar hanye ce ta fahimtar tarihi, da asali da sauran muhimman fannoni a kowace al’umma. Sai dai duk da muhimmancin wannan sashe, zamani na neman yin awon gaba da wannan bangare. Wannan nema ya sa kasashe da hukumomin kasa da kasa suke kirkiro hukumomi ko ma’aikatun kula da al’adu, wadanda ke taka rawa wajen kare abubuwan da sashen ya kunsa daga bacewa, kamar tsoffin litattafai, da sutura da abinci, da tsarin gine-gine, kide-kide da raye-raye, sana’o’i da sauransu.
A kwanakin baya ma shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci sabbin wuraren al’adun kasar Sin guda biyu, wato gidan adana tsoffin littattafai na kasar Sin, da kuma kwalejin nazarin tarihin kasar Sin.
Bayanai na nuna cewa, gidan adana tsoffin littattafai na kasar Sin, ya adana littattafai masu daraja da aka gada, wadanda suka kunshi al’adun al’ummar Sinawa. Kwalejin nazarin tarihin kasar Sin kuwa, na nazari, da yin cikakken bayani game da asalin al’adun al’ummar Sinawa.
A yayin ziyarar, shugaba Xi Jinping ya bayyana aniyarsa game da ziyarar, inda ya ce, a zamanin da muke ciki, wato zamanin dake da wadatar kasa da zaman lafiyar al’umma, ana da karfin tabbatar da al’adun al’ummar kasa.
Shugaba Xi Jinping ya dora muhimmanci sosai ga kiyaye al’adun gargajiya na al’ummar Sinawa, da gadon su, da kuma yin kirkire-kirkire da samun bunkasuwa a wannan fanni. Wannan ya kara nuna muhimmancin kiyaye al’adu, wadanda masana suka bayyana a matsayin madubin kowace al’umma. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)