logo

HAUSA

Jami’an Amurka ba za su iya dakatar da matakan sulhu na kasashen yankin Gabas ta Tsakiya ba

2023-06-07 21:17:27 CMG Hausa

Daga ranar 6 zuwa 8 ga watan Yuni ne, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ziyarci kasar Saudiyya. Wannan ita ce ziyara ta uku da wani babban jami’in Amurka ya kai kasar Saudiyya a wannan shekara.  Me ya sa suke hanzari haka? Kamfanin dillancin labaran Reuters ya yi imanin cewa, Amurka na fatan daidaita dangantakarta da kawayarta Saudiyya.

Sai dai kuma a wannan rana da Antony Blinken ya ziyarci Saudiyya, abubuwa biyu sun faru a yankin Gabas ta Tsakiya. Daya shi ne sake bude ofishin jakadancin kasar Iran a kasar ta Saudiyya. Wannan wani gagarumin ci gaba ne a alakar kasashen biyu, wato Iran da Saudiyya, bayan da suka sanar da dawo da huldar jakadanci a karkashin jagorancin kasar Sin. Wani batu kuma shi ne yarima mai jiran gado kuma firaministan Saudiyya ya gana da shugaban kasar Venezuela da ke ziyara, inda bangarorin biyu ke fatan karfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban.

Yayin da tsohuwar aminiyar Amurka ta ki mika wuya kamar yadda Amurka ta tsara, yankin Gabas ta Tsakiya mai cin gashin kanta ta kunno kai. (Ibrahim)