logo

HAUSA

Kamilla Magdeeva: Ina fatan in zama manzon mu'amalar sada zumunta tsakanin Sin da Uzbekistan

2023-06-05 19:11:26 CMG Hausa

Wata yariniyar da ta fito daga kasar Uzbekistan da ke tsakiyar Asiya, ta shafe kusan shekaru biyar tana zaune a kasar Sin, ta yaya ta shaku da Sin? Kuma me ta fahimta game da rayuwa a kasar? A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku labari ne game da wannan baiwar Allah mai suna Kamilla Magdeeva.

'Yar Uzbekistan Kamilla Magdeeva a halin yanzu karamar daliba ce da ke karatun likitanci a Jami'ar Kudu ta Tsakiya ta kasar Sin. Kamilla Magdeeva ta ce tun tana karama, kasar Sin take burge ta sosai, kuma daga lokacin ta fara sha'awar zuwa kasar Sin.

“Tuni na taba jin labarin kasar Sin a kasarmu, kuma na taba kallon fina-finan kasar Sin da yawa, inda na ga yadda kasar Sin ta samu ci gaba, gaskiya ba wai kawai kasar Sin tana da kyau ba, har ma akwai wurare masu ban sha'awa da dama da kuma kayan abinci iri-iri. A gidanmu, kawuna ya kan yaba wa kasar Sin da Sinawa, abin da ya sa nake sha'awar kasar Sin kuma na fara neman hanyoyin yin karatu a kasar Sin.”

Kamilla Magdeeva ta gaya mana cewa, wani ya ba ta shawarar cewa ta nemi gurbin karatu na gwamnatin kasar Sin, a ranar da ta karbi takardar izinin shiga jami’a, ta kusa yin kuka saboda murna.

Kamilla Magdeeva ta kara bayyana cewa, iyalinta ma suna ba ta goyon baya wajen yin karatu a kasar Sin, yin karatu a kasar Sin shi ne zabin da ya dace da ita.

Kamilla Magdeeva ta gaya mana cewa, saurin bunkasuwar kasar Sin, da dimbin al'adun tarihi, su ne manyan dalilan da suka sa ta zo nan kasar Sin don yin karatu.

“Abin da ya fi jan hankalina shi ne, dogon tarihin kasar Sin da saurin bunkasuwarta, kasar Sin tsohuwar kasa ce kuma ta zamani, ko da yake kasar Sin ta samu ci gaba cikin sauri, amma har yanzu tana rike da nata al'adu da dogon tarihi, kuma sabbin gine-ginen birane galibi suna dauke da abubuwa da dama na al'adun gargajiya. Tsoffin garuruwan kasar Sin suna da ban mamaki da kyan gani. A lokaci guda kuma akwai kyawawan wuraren shakatawa, gidajen tarihi da manyan gine-gine, ina jin kamar ina rayuwa a wani zamani na daban saboda komai yana tafiya da zamani.”

Bugu da kari, Kamilla Magdeeva ta bayyana cewa, jama'ar kasar Sin suna da kirki, kuma suna son taimako, kana yanayin tsaron jama'a a kasar yana da kyau sosai, don haka iyayenta ba su damuwa kan halinta na karatu da zama a kasar Sin.

Jami'ar Kudu ta Tsakiya tana birnin Changsha na lardin Hunan dake kudancin kasar Sin, Kamilla Magdeeva ta ce yanayin halittu, wuraren shakatawa, da kayan abinci iri-iri na birnin duk suna ba ta farin ciki sosai.

“Na fi son yanayin birnin Changsha. Birnin ya burge ni sosai, yana samun ci gaba kwarai, a wannan birnin, ana samar da sauki ga zirga-zirgar jama'a, kuma tashoshin mota da na jirgin kasa dake tafiya a karkashin kasa su ma suna kusa da makarantarmu. Akwai kuma abinci masu dadi da yawa a Changsha, duk da cewa ba zan iya sabawa da abinci mao yaji ba, idan na ga tofu mai wari wato abincin gargajiyar wurin, tabbas zan ci daya.”

A matsayinta na dalibar dake koyon likitanci, Kamilla Magdeeva tana kula da albarkatu masu yawa a fannin likitanci, da sabbin manhajoji masu inganci da kuma kyakkyawan fatan samun aikin yi a kasar Sin.

“Kasar Sin kasa ce mai samun saurin ci gaba, da karin yawan damammakin sana'o'i. Kasar Sin tana ba da ilimin likitanci mai inganci, tare da ingantattun asibitoci da kwararrun likitoci. Na sami gogewa da yawa daga malamaina, kuma ina godiya sosai a gare su, na kuma koyi amfani da sabbin kayan aikin likitanci da fasaha, kuma na sami karramawa na karanta aikin likitanci a kasar Sin.”

Baya ga karatu, Kamilla Magdeeva kuma ta bi ayarin makarantar don ziyartar yankunan karkara a lardin Hunan dake kudu maso tsakiyar kasar ta Sin, wanda hakan ya ba ta damar ganin kasar Sin mai fuskoki daban daban.  

“Na sha zuwa karkarar lardin Hunan sau da yawa, akwai gidaje masu kyau, da amfanin gona masu albarka, da murmushi a fuskokin mutanen karkara, dukkansu sun burge ni sosai. Mutanen da ke zaune a karkaran suna gaya mini cewa, rayuwarsu iri daya ce da ta birane, ko a fannin ilimi ko a fannin kula da lafiya ko kuma a fannin sayayya, yanar gizo tana saukaka komai.”

Kamilla Magdeeva ta bayyana cewa, babu shakka, kwarewar kasar Sin ta cancanci sauran kasashe su yi koyi da ita, ta yi imanin cewa, mu’ammala tsakanin kasa da kasa na bukatar koyi da juna, da samar da ci gaba a duniya tare, bayan ta kammala karatunta, ita ma tana son bayar da gudummawa kan wannan.

Ko da yake tana matashiya, amma Kamilla Magdeeva ta riga ta sami nata fahimta da tunani game da ci gaban hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu. Tana sa ran cewa, ta hanyar daukar taron koli na kasar Sin da tsakiyar Asiya da aka gudanar kwanakin baya, za a samu damammakin da Uzbekistan da Sin za su kara zurfafa hadin gwiwa don amfanar jama'ar kasashen biyu. A cewarta, kasashen Sin da Uzbekistan suna raya dangantakar dake tsakaninsu bisa daidaito da mutunta juna, kuma suna shirin aiwatar da ayyuka da dama a fannonin motoci da makamashi. Kamilla Magdeeva ta kuma yi fatan kasashen Sin da Uzbekistan za su kasance abokan juna har abada, kuma za su karfafa mu’ammala da hadin kai.

Yanzu, Kamilla Magdeeva tana shagaltuwa da karatunta a mafi yawan lokuta, ta ce tana fatan samun lokacin shirya balaguro a shekara mai zuwa, saboda kasar Sin tana da girma sosai, kuma tana son ziyartar sassan kasar.  

“Akwai kyawawan birane da yawa a kasar Sin, ina so in yi yawon shakatawa, ban taba zuwan birnin Beijing ba, ina so in je Beijing.”