logo

HAUSA

Sin za ta kara taimakawa kasashe masu tasowa da tawagogin kiwon lafiya

2023-06-02 16:53:44 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa kasashe masu tasowa da tawagogin jami’an kiwon lafiya:

 

A gabar da a yanzu haka irin wadannan tawagogin na Sin 115, ke gudanar da ayyuka a kasashen duniya 56. Mao Ning ta ce Sin za ta tallafa da matakan inganta lafiya, da kula da jin dadin al’umma a sassan duniya daban daban.

 

Jami’ar wadda ta bayyana hakan a kwanan baya yayin wani taron manema labaru, ta ce a baya bayan nan, kasashe da dama da suka hada da Laos da Cambodia, da Guinea-Bissau sun jinjinawa kwazon tawagogin tallafin kiwon lafiya na Sin.

 

Inda aka baiwa tawagogin da lambobin karramawa na kasa, da lambobin jinjinawa ta hadin gwiwa da samar da ci gaba, da dai sauransu.