logo

HAUSA

Sin na matukar son hadin kai da sauran sassan kasa da kasa a fannin nazarin sararin samaniya

2023-06-02 10:34:59 CMG HAUSA

DAGA MINA

Ran 30 ga watan nan da muke ciki, kasar Sin ta cimma nasarar harbar kumbon Shenzhou-16. Kafin an harba kumbon, mai magana da yawun hukuma mai kula da harkokin nazarin sararin samaniya ta kasar Sin ya bayyana a gun taron manema labarai na ba da bayyani kan aikin harbar kumbo na cewa, Sin na matukar maraba da ‘yan saman janati na sauran kasashe da su yi amfani da tashar Sin ta samaniya, don hadin kai wajen gudanar da ayyukan nazari, da more ci gaba tare.

Hadin kan kasa da kasa a wannan fanni, bukatun bai daya ne na kasashe daban-daban, kuma an kai ga cimma matsaya daya kan wannan lamari. Sin na nacewa ga amfani da albakatun samaniya cikin lumana, da hadin kai, da cin moriya, da kuma samun ci gaba tare, tana kuma mu’ammala da hadin kai da sauran kasashe, ko hukumomin nazarin sararin samaniya, da kungiyoyin kasa da kasa.

A nahiyar Afirka kuwa, hadin kan bangarorin biyu ya zama karfin ingiza hadin kansu, karkashin dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika, da shawarar “ziri daya da hanya daya”. Bangarorin biyu sun yi hadin kai a fannin fitar da tauraron dan Adama da aka harhada, da kafa manyan na’urorin ayyukan nazarin sararin samaniya, da more albarkatu, da nazarin tauraron dan Adam, tare da cimma nasarori da dama.

Kimiyya da fasaha a wannan fanni, sun kara karfin zamanintar da al’umma da tattalin arzikin Afrika, har ta kai jama’arsu suna cin gajiya a zaman rayuwarsu na yau da kullum.

Dan saman janati na farko da ya taka doron duniyar wata Neil Alden Armstrong, ya taba nuna cewa, ci gaban da ya samu a fannin nazarin sararin samaniya karamar nasara ce, amma babban ci gaba ne ga dan Adam. Nasarorin da Sin take samu a wannan fanni, ba ma kawai ci gaban da Sin take da shi ba ne, har ma ya taka rawa ga kokarin da daukacin Bil Adama suke yi na nazarin sararin samaniya. Sin na nacewa ga matsayin nazarin sararin samaniya cikin lumana, ta hadin kai da sauran sassan kasa da kasa, ta yadda daukacin bil Adama za su more wannan ci gaba. (Mai zana da rubuta: MINA)