logo

HAUSA

Shahararrun ‘yan wasan kwallon tebur Sun da Fan sun zama zakarun wasan na duniya

2023-06-01 20:05:17 CMG Hausa

Shahararrun ‘yan wasan kwallon tebur na kasar Sin Sun Yingsha, da Fan Zhendong, sun zama zakarun wasan na duniya ajin mata da na maza, a gasar da hukumar ITTF ke shiryawa mai lakabin WTTC, a karshen makon jiya a birnin Durban na Afirka ta kudu.

Bayan dukkanin wasannin rukunoni na kasar Sin da Sun ta buga, a wasan karshe na birnin Durban, ta kai matsayin farko ajin ‘yan wasa daidaiku, bayan ta doke mai rike da kambin wasan Chen Meng da maki 4 da 2, yayin da a ajin maza Fan ya yi nasarar ci gaba da rike kambin sa, bayan ya doke abokin karawar sa Wang Chuqin da ci 4 da 2.

Da wannan nasara, ‘yan wasan kwallon tebur na kasar Sin ajin mata dake buga gasar daidaikun ‘yan wasa, sun ci gaba da rike kambin gasar na duniya a karo na 15 a jere, tun bayan karbar kambin a shekarar 1995.

Baya ga Sun da ta lashe lambar zinari a gasar, mai biye mata Chen Xingtong ita ma daga kasar Sin ta lashe lambar tagulla a gasar, yayin da ita ma ‘yar wasan daga kasar Japan Hina Hayata ta lashe lambar tagulla.

A bangaren gasannin ajin maza kuwa, wannan ne karo na 10 da kasar Sin ke ci gaba da lashe gasar daidaikun ‘yan wasan kwallon tebur tun daga shekarar 2005. Baya ga dan wasa Fan Zhendong da ya lashe lambar zinari, su ma ‘yan wasan Sin Ma Long da Liang Jingkun, sun lashe lambar tagulla a gasar ta hukumar ITTF.

Game da yadda gasar ta bana ta gudana, shugabar hukumar kwallon tebur ta kasa da kasa ITTF Petra Sorling, ta ce gasar ta bana ta kayatar, tana kuma alfahari da yadda komai ya tafi lami lafiya. Ta ce "Ina alfahari da irin tasirin da kwallon tebur ke iya yi. Ina alfahari da yadda daukacin masu son wannan wasa suka amince da Afirka ta kudu wajen karbar bakuncin gasar ta bana. Afirka ta kudu ta karbi wannan kalubale yadda ya kamata. Ina fatan hakan zai kara janyo hankalin sabbin ‘yan wasan kwallon tebur zuwa kasar a nan gaba".

Petra Sorling ta kara da cewa, gasar ta bana ta kafa tarihi mai ban sha’awa. Kuma ko shakka ba bu hakan zai zaburar da karin sabbin ‘yan wasan kwallon tebur wajen shiga a dama da su a wannan wasa. Ta ce “Ina fatan yara kanana da dama sun kalli wannan gasa, kuma hakan zai karfafa gwiwar su wajen shiga wasan kwallon tebur a nan gaba. Gabatar da wannan gasa a nan Durban, ya wuce batun wasa kadai, domin kuwa ya shaida irin kwazon mu na yayata kaunar kwallon tebur zuwa ga dukkanin nahiyoyi da al’adu".

Sorling ta ce duk inda suka kai gasar kwallon tebur, musamman a yanzu da suke kai gasar wurare da ba ta taba zuwa ba, suna kara bayyana wasan ga karin jama’a, domin ta hanyar yayata wasan ne kadai za a iya raya shi yadda ya kamata. Ta ce fatan su shi ne samun karin ‘yan kallo. Ta ce “A lokaci guda kuma, mun san cewa idan aka kai wasa sabbin kasuwanni, yana daukar lokaci kafin mutane su waye da kayatarwar sa”.

Gasar bana, ita ce ta farko da ta gudana a nahiyar Afirka cikin shekaru 84 da fara gudanar da ita. Kuma a ranar Alhamis din makon jiya, dan wasan kasar Masar Omar Assar, ya kafa tarihin kasancewa na biyu daga nahiyar Afirka, baya ga dan wasan Najeriya Quadri Aruna, da ya kai ga zagayen wasan kusa da kusan na karshe, kafin hakan, Quadri Aruna ya kai ga wannan matsayi a gasar da aka buga a birnin Houston na Amurka shekaru 2 da suka gabata.

A nasa tsokaci, game da yadda gasar ta bana ta gudana kuwa, shugaban hukumar kwallon tebur ta Afirka ta kudu Yusuf Carrim, cewa ya yi hukumar su ta sanar da karewar tikitin wasanni 2 na karshe na gasar da aka buga a kasar, tun kafin zuwan ranaikun wasannin, hakan a cewar sa ya yi matukar ba da mamaki.

Carrim ya ce "Mun yi matukar alfahari da hakan. Mun yi farin ciki sosai. Abun da ya faru ya nuna kwazon mu, ya kuma nuna komai mai yiwuwa ne, kuma akwai yiwuwar dan wasa daga nahiyar Afirka ya kai ga lashe gasar nan ba da jimawa ba.

Jami’in ya kara da cewa, gudanar da gasar kwallon tebur ta kasa da kasa a birnin Durban, ya yi daidai da manufar ITTF ta mayar da wasan zama na dukkanin duniya. Zan yi amfani da wannan dama wajen mika sako na na fatan alheri, ga daukacin iyalan wasan kwallon tebur, bisa nasarar kawo wannan babbar gasa zuwa kasar mu. Yanzu haka muna kan turbar mayar da kwallon tebur babban wasa a kasar mu”.

A nasa bangare kuwa, babban jami’in sassan hukumar ta ITTF Steve Dainton, cewa ya yi nasarar da Assar ya cimma a gasar ta kayatar. Kuma abun da suke fatan gani ke nan a wannan gasa. Wato samun karin ‘yan wasa daga sassa mabanbanta su rika shiga gasanni iri iri.

Dainton ya ce yayin gasar kasa da kasa ta shekarar 2027 ajin daidaikun ‘yan wasa da za a gudanar, suna fatan sake zuwa wani bangaren na duniya. Ya ce “Muna fatan zuwa karin wasu kasuwannin na daban, ko na Amurka ta kudu ko Oceania, saboda hakan zai zama wata babbar dama ta yayata wasan ga sauran sassa. Fatan mu shi ne wasan ya karade dukkanin sassan duniya".