logo

HAUSA

Gudummawar Kasar Sin Ga Aikin Tabbatar Da Zaman Lafiya A Duniya Abu Ne Da Ake Gani A Zahiri

2023-05-31 20:14:14 CMG Hausa

A ranar 29 ga watan Mayu ne aka yi bikin ranar jami’an wanzar da zaman lafiya ta MDD na bana. Kudiri mai lamba 57/129 na babban taron MDD ne ya ayyana wannan rana a ranar 11 ga watan Disamban, shekarar 2002.

Bayanai na nuna cewa, an gudanar da aikin tabbatar da zaman lafiya na MDD na farko a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 1948, lokacin da kwamitin sulhun MDD ya amince da tura wata karamar tawagar sojoji zuwa yankin gabas ta tsakiya a matsayin masu sanya ido kan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Isra’ila da kasashen Larabawa dake makwabtaka da ita.

Kasar Sin ita ce kasa ta biyu dake biyan kudin tallafi da kudin karo karo ga MDD yadda ya kamata, kuma ita ce kasar da ta fi kowacce ba da adadi mai yawa na dakarun wanzar da zaman lafiya, tun daga shekarar 1990.

Haka kuma, Sin ta aike da dakarun da yawansu ya kai sama da dubu 50, cikin shekaru 30 da suka gabata. Dakarun wanzar da zaman lafiya na kasar Sin suna gudanar da ayyukan daidaita rikici da kiyaye kwanciyar hankali da kuma ingiza ci gaban tattalin arziki a kasashe da yankuna sama da 20, ciki har da Cambodiya, da Kongo(Kinshasa), da Liberiya, da Sudan, da Lebanon, da Sudan ta kudu, da Mali, da Afirka ta tsakiya da sauransu.

A halin yanzu, jami’an wanzar da zaman lafiya na kasar Sin sama da 2500 suna ci gaba da gudanar da ayyuka a wurare daban-daban da kuma hedkwatar MDD. Wannan ya kara shaida kudirin kasar na neman ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali da ma ci gaba sun samu a duniya baki daya.

A yayin da ake amfani da wannan rana, wajen tuna gudummawar da masu kayan sarki da fararen hula, wadanda suka kwanta dama yayin da suke aikin wanzar da zaman lafiya, mataimakin babban sakataren MDD mai kula da harkokin kiyaye zaman lafiya Jean-Pierre François Renaud Lacroix ya bayyana cewa, yana alfahari sosai da yadda aka gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD har na tsawon shekaru 75, kana ya yabawa kasar Sin kan yadda ta samar da muhimmiyar gudummawa ga sha’anin kiyaye zaman lafiya na MDD.

Jean-Pierre Lacroix ya ce, Sin ta kasance mai goyon bayan MDD wajen gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya, kana ta samar da gudummawa sosai ga ayyukan. Ya kuma bayyana cewa, kasashe da dama sun samu zaman lafiya da kwanciyar hankali sanadiyyar ayyukan kiyaye zaman lafiya, lamarin da ya shaida cewa, ayyukan suna da amfani.

Don haka, yana fatan a nan gaba, MDD da Sin za su kara hadin gwiwa kan ayyukan kiyaye zaman lafiya. Abubuwan da Sin take gudanarwa abu ne da ake ganinsu a zahiri ba maganar fatar baki ba. (Ibrahim Yaya)