logo

HAUSA

Sashen Hausa na CRI ya cika shekaru 60 da watsa labarai da harshen Hausa

2023-05-31 08:51:03 CMG Hausa

A bana ne, sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin, ya cika shekaru 60 cif da watsa labarai cikin harshen Hausa. An kafa sashen ne a shekarar 1961, ya kuma fara watsa labarai a shekarar 1963. Daga wancan lokaci zuwa yanzu, sashen ya yi nasarar ilimantar da masu sauraro a sassan duniya game da kasar Sin da al’ummar Sinawa.

Haka kuma sashen ya taimaka wajen kara fahimtar da masu sauraro ci gaban kasar Sin da rawar da kasar ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, da alakar Sin da sauran kasashe musamman kasashe masu tasowa.

Ba ya ga shirye-shiryen rediyo, sashen yana kuma watsa shirye-shirye ta kafofin sadarwar zamani irinsu Facebook da sashensa na intanet, domin dacewa da zamani, inda masu bibiyarsa ta wadannan kafofi suka tasamma miliyan da doriya. Albarkacin wannan rana, sashen Hausa na CRI, yana maraba da sakonninku kan yadda za mu kara inganta shirye-shiryen da muke kawo muku. (Saminu,Ibrahim/Sanusi Chen)