logo

HAUSA

Dai Zhengqin: soja Basiniya mai kawar da nakiyoyin da aka binne a Lebanon

2023-05-30 19:16:52 CMG Hausa

 

Dai Zhengqin, daliba ce a birnin Suzhou na lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin. Ta taba sha’awar shiga soja. A watan Agustan shekarar 2021, ta je kasar Lebanon a matsayin soja mace mai kiyaye zaman lafiya na kasar Sin, inda ta dauki shekara guda tana aikin kawar da nakiyoyin da aka binne a kasar. Ta yi fice sosai a aikinta, don haka aka ba ta lambar yabo na zaman lafiya na MDD. A watan Satumban shekarar 2022, ta kammala aikinta cikin nasara, ta koma karatu. (Tasallah Yuan)