logo

HAUSA

Wajibi Ne Japan Ta Sauke Nauyi Dake Wuyanta Kan Zuba Dagwalon Ruwan Nukiliya Cikin Teku

2023-05-30 20:43:38 CMG Hausa

Yayin da kasar Japan take dab da zuba dagwalon ruwan nukiliya cikin teku, Vincent Kelly, mazaunin wani tsibiri da ke tekun Pasifik ya kara bayyana damuwa, yana mai cewa, shirin Japan na zuba dagwalon ruwan nukiliya cikin teku, kuskure ne, wanda zai haifar da bala’i.

Ana fatan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa wato IAEA da ke ziyara a Japan za ta yi bincike bisa sanin ya kamata, da adalci, a matsayin kwararriya, kan aikin Japan na zuba dagwalon ruwan nukiliya cikin teku, a kokarin kiyaye tsaron kasa da kasa.

Tun daga jiya 29 ga wata, kwararrun hukumar IAEA suka fara ziyararsu ta kwanaki 5 a Japan. Kafofin yada labaru na Japan sun ruwaito cewa, wannan ne karo na karshe da hukumar za ta yi bincike kan aikin zuba dagwalon ruwan nukiliya cikin teku, kafin ta gabatar da rahoton nazarinta na karshe.

Rafael Mariano Grossi, babban sakataren IAEA ya bayyana a fili yayin da ya ziyarci kasar Sin a kwanan baya cewa, hukumar ba ta amince ba, kuma ba ta goyon bayan shirin duk wata kasa na zuba dagwalon ruwan nukiliya cikin teku, kuma ba za ta yarda da ayyukan da suka saba wa mizanin tsaro na duniya ba. Yayin da kasashen duniya ke kin yarda da kuma nuna shakku kan shirinta na zuba dagwalon ruwan nukiliya cikin teku, bai kamata gwamnatin Japan ta nemi samun iznin zuba dagwalon ruwan nukiliya cikin teku daga wajen hukumar IAEA ba.

Yau shekaru 12 da suka gabata, hadarin nukiliya na Fukushima ya haifar da babban bala’i ga duniya. Yanzu Japan tana yunkurin illata moriyar bai daya ta daukacin bil’Adama, domin samun moriyarta ta gajeren lokaci. Dole ne a ki yarda da abin da Japan take yi. Kamata ya yi Japan ta sauke nauyin dake wuyanta, ta tattauna da kasashe makwabtanta da hukumomin kasa da kasa masu ruwa da tsaki, domin cimma daidaito. Kafin haka kuma, kada Japan ta yi gaban kanta wajen zuba dagwalon ruwan nukiliya cikin teku. (Tasallah Yuan)