logo

HAUSA

Sojojin Sudan da dakarun RSF sun amince da tsawaita wa’adin tsagaita bude wuta na kwanaki 5

2023-05-30 09:39:33 CMG Hausa

Rahotanni daga Sudan na cewa, sojojin kasar da dakarun kai dauki na gaggawa na kasar (RSF) sun amince da tsawaita wa’adin yarjejeniyar tsagaita bude wuta da suka sanyawa hannu a ranar 20 ga watan Mayu a birnin Jeddah na kasar Saudiyya da kwanaki biyar.

Bangarorin biyu sun jaddada kudurin baiwa fararen hula damar ficewa lami lafiya daga yankunan da ake rikici da kuma kare kayayyakinsu.

An cimma yarjejeniyar tsagaita bude wutar ce ta gajeren lokaci da kuma shirye-shiryen jin kai ta hanyar shawarwarin da aka fara a ranar 6 ga Mayu, bisa shiga tsakanin kasashen Saudiyya da Amurka, da nufin kawo karshen rikici a Sudan da kuma saukaka shigar da kayan agaji ga fararen hula.

Yarjejeniyar ta kwanaki bakwai, wadda ta fara aiki a ranar 22 ga watan Mayu, an shirya za ta kare ne da karfe 9 da mituna 45 na daren jiya, agogon kasar.

Ko da a jiya Litinin ma, fada ya sake barkewa a birnin Khartoum na kasar Sudan, tsakanin sojojin kasar da dakarun RSF, sa’o’i kadan kafin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin bangarorin biyu. (Ibrahim)