logo

HAUSA

An cimma nasarar harba kumbon Shenzhou-16 dauke da ‘yan sama jannati 3

2023-05-30 10:31:13 CMG Hausa

Da sanyin safiyar yau Talata ne aka yi nasarar harba kumbon Shenzhou-16 dauke da ‘yan sama jannati 3, inda ake sa ran amfani da kumbon wajen gudanar da ayyuka da dama cikin watanni 5.

An dai harba kumbon ne ta amfani da rokar Long March-2F, daga tashar harba kumbuna ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin. Kuma bisa tsarin aikin su, ‘yan sama jannatin Shenzhou-16 za su gudanar da manyan ayyukan gwaje-gwaje na kewayen falaki, da sauran gwaje gwaje a fannoni daban daban.

Kumbon dai na dauke da ‘yan sama jannati Jing Haipeng, da Zhu Yangzhu da Gui Haichao, wadanda za su ganewa idanun su lokacin turke kumbon Tianzhou-5 na dakon kayan, da Shenzhou-17 mai dauke da ‘yan sama jannati, da ma lokacin da kumbon Shenzhou-15, da Tianzhou-5 masu dauke da ‘yan sama jannati za su rabu da turken su.

Bayan harba kumbon Shenzhou-16, da misalin karfe 6:42 na safiyar yau Talata, an gudanar da shagalin bikin murnar harba Shenzhou-16, a tashar Jiuquan ta harba taurarin dan adam.  (Saminu Alhassan)