logo

HAUSA

Sin za ta kara taimakawa kasashe masu tasowa da tawagogin kiwon lafiya

2023-05-30 09:46:16 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa kasashe masu tasowa da tawagogin jami’an kiwon lafiya, a gabar da a yanzu haka irin wadannan tawagogin na Sin 115, ke gudanar da ayyuka a kasashen duniya 56. Mao Ning ta ce Sin za ta tallafa da matakan inganta lafiya, da kula da jin dadin al’umma a sassan duniya daban daban.

Jami’ar wadda ta bayyana hakan a jiya Litinin, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da take amsa tambayar da aka yi mata game da batun, ta ce a baya bayan nan, kasashe da dama sun jinjinawa kwazon tawagogin tallafin kiwon lafiya na Sin.

A Guinea-Bissau, shugaban kasar Umaro Sissoco Embalo, ya baiwa tawagar jami’an lafiya ta Sin dake aiki a kasar lambar karramawa ta kasa, da lambar jinjinawa ta hadin gwiwa da samar da ci gaba.

Kaza lika ita ma tawagar jami’an jinyar cutar COVID-19 ta amfani da magungunan gargajiyar kasar Sin, ta karbi lambar jarumta ta gwamnatin Cambodia, wadda ma’aikatar lafiyar kasar ta mika mata.  (Saminu Alhassan)