logo

HAUSA

Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Kawo Karshen Rikicin Ukraine A Siyasance

2023-05-30 17:04:03 CMG Hausa

Kasar Sin ta hannun wakilinta na musammam mai kula da harkokin Turai da Asia, Li Hui, ta yi tuntuba mai zurfi da ma musayar ra’ayi da dukkan bangarori, game da warware rikicin Ukraine a siyasance.

 A ra’ayina, wannan yunkuri ya sake tabbatar da matsayin kasar Sin na son ganin tabbatuwar zaman lafiya a duniya da kaucewa goyon bayan wani bangare ko ruruta wutar rikicin.

Zuwa yanzu, an ga yadda mummunan tasirin rikicin na Ukraine ya bazu zuwa sassan duniya, tare da jefa al’ummomin da ba su ji ba, ba su gani ba cikin rudani.

Tun bayan barkewar rikicin, ake kokarin shafawa kasar Sin bakin fenti, cewa wai ta na goyon bayan wani bangare, sai dai, muradin Sin a ko da yaushe shi ne, tabbatar da wanzuwar zaman lafiya. Kuma ziyarar Li Hui kasashen Ukraine da Poland da Faransa da Jamus da Rasha da hedkwatar EU, ya tabbatar da hakan, domin ya tuntubi dukkan bangarori ba tare da ware wani ba. Adalci shi ne sauraron ra’ayin kowanne bangare tare da kokarin samar da maslahar da za ta karbu ga kowa, cikin ruwan sanyi ba tare da zubar jini ba.

Maimakon marawa Sin baya wajen yi wa tufkar hanci tare da fitar da duniya daga halin da ta shiga, kasashen duniya dake kiran kansu manya, sun nuna karara cewa, ba sa kaunar zaman lafiya ko kwanciyar hankalin duniya. An ga yadda tun bayan barkewar rikicin, Amurka da kawayenta ke ci gaba da samar da makaman yaki ga Ukraine, tare da kakabawa Rasha takunkumai. Ko a baya bayan nan, sun tashi taron kungiyar G7 da matakan kara sabbin takunkumai kan Rasha.

Shi wannan ba bangaranci ba ne? Shin makaman da suke samarwa ba zubar da jini da asarar rayuka za su haifar ba? Shin takunkuman da suke sanyawa, ba kunchin rayuwa za su haifar ga al’umma ba?.

Ba sai an fada ba, hanyar da kasar Sin ta dauka ita ce za ta kai ga samar da zaman lafiya da takaita asarar rayuka da dukiya.  Yayin da tallafin soji da takunkumai za su kai ga ci gaban yaki da asarar rayuka da kara dagula yanayin duniya. (Fa’iza Mustapha)