logo

HAUSA

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya ce gina sabuwar Najeriya shine babban burin sa

2023-05-30 09:25:05 CMG Hausa

A jiya Litinin 29 ga wata aka gudanar da bikin rantsar da Bola Ahmad Tinubu a matsayin sabon shugaban tarayyar Najeriya bayan karewar wa`adin tsohon shugaba Muhammadu Buhari.

A jawabin sa na bayan rantsuwa, sabon shugaban na Najeriya yace, yana da manufofi masu  kyau ga `yan kasa, kuma zai sanya Najeriya a gaba domin fito da ita daga halin da ta shiga na koma bayan tattalin arziki da tsaro ,da kuma rashin nuna kishin kasa a tsakanin wasu al`ummomin kasar.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shugaba Bola Ahmad Tinubu wanda ya kasance shugaban tarayyar Najeriya na 16 a jerin shugabannin da suka jagoranci kasar tun bayan samun mulkin kai, ya ce yana da yakinin cewa ‘yan Najeriya za su fuskanci sabuwar rayuwa ta farin cikin da yaduwar arziki.

Ya cigaba da cewa gwamnatin sa zata kasance mai tuntuba a ko da yaushe da nufin warware duk wasu matsalolin da suka jima suna ci wa al`umma tuwo a kwarya, ya ce ba burin sa ba ne zartar da wata manufa bisa ra`ayin kansa.

Yace zai gudanar da mulkin sa tare da al`umma, domin sai an hada hannu tare da nuna kishin kasa Najeriya zata iya kaiwa ga babban mastayi a tsakanin kasashen duniya.

A kan mahimman abubuwan da gwamantin sa zata fi baiwa fifiko kuwa, sabon shugaban na tarayyar Najeriya ya fara ne da cire tallafin man fetur wanda sanadiyar sa buliyoyin dalar Amurka ke zurarewa a aljihun wasu tsirarun mutane a duk shekara

“Maimakon hakan yanzu za mu juya akalar kudin tallafin domin zuba jari a bangarorin samar da ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya da samar da akin yi wadanda duka zasu taimakawa rayuwar miliyoyin al`umma”

Akan batun tattalin arziki kuwa Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya nanata kudirin sa na kara yawan karfin tattalin arzikin cikin gida wanda sannu a hankali zai rage matsalolin rashin aikin yi.

Ta banaren tsaro kuma sabon shugaban na tarayyar Najeriya yace gwamnatin sa zata sake fasalin tsarin tsaron kasa da kuma kyautata sha`anin shari`a wanda hakan zai rage matsalolin tashe-tashe hankula a tsakanin al`umma da kuma ayyukan ta`addanci.

“Zamu saka jari sosai wajen samar da Karin jami `an tsaro, da ba su horo da samar masu da wadatattun kayan aiki da biyan su hakkokin su a kai a kai.”

Ha`ila yau shugaba Tinubu ya kara da cewa za a kyautata harkokin masana`antun cikin gida ta yadda Najeriya zata rage dogaro da kayyakin da ake shigowa da su daga waje.

Akan batun wutar lantarki kuwa, ya ce zai yi bakin kokarin ganin `yan Najeriya na samun wadatacciyar wuta kuma kan farashin mai saukin gaske, za a cimma hakan ne kamar yadda ya fada ta hanyar kyautata sha`anin samar da wutar da kuma dakon wutar zuwa sassan kasar daban daban.

Ta fuskar noma kuwa, shugaba Bola Ahmad Tinubu ya ce za a fito da tsare tsare da za su saukakawa manoma wajen noman amfanin gona tare da fito da hanyoyin adana kayan amfanin nasu domin kaucewa lalacewa da kuma rage farashin kayan a kasuwanni, haka zalika za a samar da sabbin hanyoyin kiwon dabbobi kamar yadda yake a sauran kasashe da nufin maganin tashe tashen hankula akan filaye da mashayar dabbobi.

Ta fuskar manufar sa ga kasashen waje kuwa, sabon shugaban na tarayyar Najeriya ya ce babban burin sa shi ne tabbatar da samun dauwamammen zaman lafiya a kasahen yammacin Afrika da ma Nahiyar baki daya, ya ce zai yi aiki tare da kungiyar ECOWAS da ta AU da sauran hukumomi da kungiyoyin kasa da kasa duk domin dakile rikice rikice da kuma kare afkuwar su a Nahiyar Afrika baki daya.(Garba Abdullahi Bagwai)