Bashir Yakubu Sani: Abubuwa da dama sun burge ni a kasar Sin
2023-05-30 15:41:36 CMG Hausa
Bashir Yakubu Sani, dalibi dan asalin Kanon tarayyar Najeriya ne, wanda a yanzu haka yake karatun digiri na biyu a wata jami’ar da ake kira Capital University of Economics and Business, wato jami’ar koyon ilimin tattalin arziki da kasuwanci ta Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
A zantawar sa da Murtala Zhang, Malam Sani wanda ya shigo kasar Sin tun bara, ya bayyana abubuwan da suka burge shi, musamman yadda Sinawa ke bin tsari da doka. Haka kuma ya ce, yadda kasar Sin ta iya tsara manufofin raya tattalin arziki da kasuwanci ya ba shi sha’awa matuka, kuma abun koyi ne mai ma’ana. (Murtala Zhang)