Ya dace Amurka ta koyi hikimomin Kissinger don yin mu’amala da kasar Sin
2023-05-29 13:25:49 CMG Hausa
A matsayinsa na sakataren harkokin waje mafi jawo hankali a tarihin kasar Amurka, Dokta Henry Alfred Kissinger ya cika shekaru 100 a duniya.
A tarihin ayyukan diflomasiyyar sa, ziyarar sirri da ya kai Beijing a shekara ta 1971 na da muhimmanci sosai, inda shi da shugabannin Sin da Amurka na wancan lokaci, suka cimma nasarar farfado da dangantakarsu, duk da cewa tsare-tsaren su ba iri daya ba ne. Har yanzu wannan shiri yana da wani muhimmin tasiri ga Sin da Amurka da ma duniya baki daya.
Dr. Kissinger ya ba da shawarar tuntubar juna da yin hadin gwiwa da kasar Sin, don kulla hulda tsakanin Sin da Amurka bisa samun moriyar juna, kuma ya yi imanin cewa yin hakan yana da alfanu ga Amurka, a kokarin kafa wata hulda dake amfanawa juna, kana a ganin sa, hakan ya dace da muradun Amurka. Hakikanin gaskiya, abu na farko da ya dace ‘yan siyasar Amurka su koya shi ne, yadda za su fahimci muradun kasarsu, da kara fahimtar cewa, kiyaye muradun kasar su, ba ya nufin dole a nuna kiyayya ga kasar Sin, tare da kawo wa ci gaban ta tsaiko.
Kwanan nan a wata hira da ya yi da mujallar Economist, Kissinger ya ce: “Shin akwai yiwuwar Sin da Amurka za su zauna lafiya tare ba tare da yi wa juna barazanar kaddamar da yaki ba? Haka nake tunani a baya, hakan ma yanzu nake tunani.”
Ana fatan mahukuntan Amurka su koyi hikimomin magabata, da tsara manufofi kan kasar Sin masu ma’ana yadda ya kamata, saboda hakan ya dace da babbar moriyar kasashen biyu da ma duniya baki daya, wanda kuma wata kila zai zama kyautar da Dokta Kissinger ke matukar sa ran gani yayin da yake murnar cikar sa shekaru 100 a duniya. (Murtala Zhang)