logo

HAUSA

Manzon musamman na shugaba Xi Jinping zai halarci bikin rantsuwar sabon shugaban Nijeriya

2023-05-29 17:16:53 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta sanar a yau Litinin cewa, bisa gayyatar da gwamnatin kasar Nijeriya ta yi masa, manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping kuma mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Peng Qinghua zai halarci bikin rantsuwar sabon shugaban kasar Nijeriya Bola Tinubu da za a yi a birnin Abuja a yau.

Ban da wannan kuma, yayin da Mao Ning ta amsa tambayoyi game da makomar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, ta bayyana cewa, a halin yanzu, ana fuskantar kalubale a duniya, kuma a matsayin kasa mai tasowa mafi girma da nahiyar da ta fi samun kasashe masu tasowa, Sin da Afirka sun fi bukatar kara hadin gwiwa da juna. Ta ce Sin tana son yin kokari tare da kasashen Afirka, da bin ra’ayin bangarori daban daban, da tabbatar da moriyarsu, da sa kaimi ga zamanintar da su, da yin kwaskwarima kan tsarin sarrafa harkokin duniya, da neman samun tsaro, da yin mu’amalar al’adu da juna, da gina al'ummomin Sin da Afirka mai makoma ta bai daya, da kuma zama misali na raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’Adama. (Zainab)