logo

HAUSA

Emily: Na samu damar cimma buri na a kasar Sin

2023-05-29 20:18:56 CMG Hausa

Emily matashiya ce da ta fito daga kasar Brazil. Tun da farko ta koyi Sinanci da kanta, har ta zama almajira mai gadon al'adun gargajiya na kasar Sin, wato rera Jingdong Drum. Labarinta yana cike da fara'a ta kasar Sin. To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau za mu kawo muku labari ne game da wannan baiwal Allah mai suna Emily.

“Lokacin da Sinanci ya fara shiga rayuwata, sai rayuwata ta yi kamar furannin peonies masu budewa a cikin watan Mayu.”

Emily ‘yar birnin Franca na kasar Brazil, a halin yanzu tana karatun dangantakar kasa da kasa a Jami'ar Nankai da ke birnin Tianjin na kasar Sin, kamar yadda Emily ta ce, ta gamu da Sinanci ba zato ba tsammani ne a daidai watan Mayu, lokacin da peonies suke yin fure.

“Lokacin da nake makarantar sakandare, wata rana da yamma sai na ga wata malamar kasar Sin da ke koyar da dalibai a aji. Sinancin da ta rubuta a kan allo cike da sihiri da kayatarwa. Wannan malamar kasar Sin tana da son jama’a sosai, kuma ita ce Basiniya ta farko da na hadu da ita, kuma kyakkyawan yanayinta, da murmushinta mai ban sha’awa suna sa mutane son kusantarta, da fahimtar ta. Dalibai da yawa suna son azuzuwanta, ciki har da ni.”

A cewar Emily, a lokacin ne ta fara nuna sha'awar Sinanci, da al'adun kasar Sin sosai. Ta ce tana son Sinanci sosai, kuma Sinanci ya canza rayuwarta.

Daga koyon Sinanci da kanta, har zuwa lokacin da ta zama fitacciyar daliba a kwalejin Confucius, Emily ta yi nasarar neman gurbin karatu na farko a jami'ar Nankai, bisa jajircewarta, da kuma tsayawar da take yi kan cimma burinta. A watan Satumba na shekarar 2018, ta zo kasar Sin daga Brazil, kuma ta fara wata sabuwar tafiya ta cimma burinta a Jami'ar Nankai.

“Na yi matukar farin ciki da samun damar zuwa kasar Sin don yin karatu, daga karshe na samu damar cimma buri na, ko kuma dai, na soma kokarin tabbatar da mafarki na.”

Ga yadda Emily ke rera Jingdong Drum, wata irin al'adar gargajiya ce ta kasar Sin. Wannan sananniyar salon fasahar gargajiya ce da ke samun karbuwa sosai a wajen jama'ar dake arewacin kasar Sin.

Emily ta ce a karon farko da ta saurari Jingdong Drum da aka rera, sai wannan fasahar rera waka ta burge ta sosai. Daga baya, ta koyi fasahar a wurin malami, har ma ta zama almajira magajiyar al’adun gargajiya na Jingdong Drum.

Yayin da take rera wakar a kan dandali, Emily tana kara nuna sha’awa kan kyawun sauti, da kade-kaden ganguna, da halin fasahar kidan Rap na kasar Sin.

“Rera Jingdong Drum kamar yin magana ne, kuma a lokaci guda ana bugun ganga tare, wata irin fasahar kidan Rap ce ta jama'ar Sin. A kasarmu ta Brazil, mu ma muna da fasahar ganga, ganga ta Brazil, ganga ce mai sauti kamar kuna so ku yi rawa a bikin carnival, amma sautin gangar Jingdong na sanya mutane su ji ba sa son yin komai sai saurare, da kuma jin dadin sautin a hankali. Kamar sauran al'adun gargajiyar kasar Sin masu yawa, za ta burge mutane sosai, kuma za ta shiga cikin zukatanmu.”

Emily ta ce, ta hanyar zuwa wurare daban-daban don halartar wasan kwaikwayo tare da malaminta, ta sami damammaki da yawa na koyon al'adun kasar Sin, da sanin yanayin rayuwar Sinawa, da jin hakikanin ma'anar al'adun kasar ta Sin.

A kasar Sin, Emily na son yawo kan tituna, da jin dadin ainihin halin rayuwar Sinawa, da kuma jin yanayin wadata da yalwar rayuwar su.

“Ina son zuwa kasuwa sosai, za ka iya sanin yadda rayuwar jama'ar kasar Sin take idan ka zo kasuwa mai kayatarwa, domin ainihin halin zaman rayuwar Sinawa ya wanzu a cikin 'radish da kabeji', 'abinci da kuma abin sha'.”

Baya ga haka, Emily ta kuma ji niyya, da hikimar jama'ar kasar Sin na kawar da talauci da samun wadata. Ta ce, Sinawa sun samu hanyar raya kasa ta "zama cikin jituwa tare da yanayin halittu", kuma a hakika gwamnatin kasar Sin tana kokarin taimakawa jama'arta, wajen neman jin dadi da alheri.

“Na taba zuwan kauyen Daduzhuang da ke birnin Tianjin na kasar Sin, an ce a da akwai wasu kananan masana’antu ne kawai a kuayen, kamar masana'antar kera sassan injin motoci da sauransu, kuma yanayin kauyen ba shi da kyau sosai. Daga baya, a karkashin jagorancin jami’an kauyen, mazauna wurin sun fara dasa duma iri daban daban, wanda suka hada da duman Mexico, da wasu masu kuraje da dai sauransu. Kayayyakin da ake sarrafawa daga duma suna samun karbuwa sosai, domin a kasar Sin, ma’anar duma na nufin albarka, kuma alama ce ta arziki da wadata. Gaskiya gwamnatin Sin tana da karfi sosai, kuma tana iya taimakawa jama'arta sosai.”

Har ila yau, Emily ta taba zuwa gundumar Zhuanglang, ta lardin Gansu dake arewa maso yammacin kasar Sin, a matsayin malama mai ba da taimako, don sanin yadda ake samun ci gaban ba da ilmi na tushe a yankunan karkara, a yayin da ake kokarin farfado da karkara a kasar ta Sin. Ta ce,

“Daga idanun dalibai na, na tuna da ranar da malamar Sinamci ta kwalejin Confucius ta zo makarantarmu, don gabatar da al'adun kasar Sin a yayin da nake karatu a karamar sakandare. Ita ce ta zaburar da ni zuwa kasar Sin don yin karatu. Yanzu lokaci ya yi da nake zaburar da wadannan yara su tafi waje don fahimtar wurere daban daban.”

Emily ta ce, a ganinta wannan ita ce hanyar yin musanya da gadon al'adu. Mutane suna nuna yabo ga juna kuma suna samun ci gaba tare, wannan shi ne abin da Sinawa ke kira koyo da juna a fannin al’adu tsakanin al'ummomi.

Ga Emily, shekaru biyar da ta yi a kasar Sin sun cika da ma'ana, ta ce za ta ci gaba da karatu a kasar Sin, kuma za ta yi amfani da abin da ta koya wajen karfafa abokantaka a tsakanin Brazil da Sin.

“Na koyi abubuwa da yawa a kasar Sin, tun daga tarihi da al'adun kasar Sin, zuwa ra'ayoyi da shawarwari na kasar Sin. Sin ta sa na bude idannu, ta kuma koya mini gaskiya da yawa. Har yanzu kawai abubuwa da yawa dake bukatar in koya, kuma na soma kokarin cimma buri na ba da dadewa ba. Duk abun da zan yi a nan gaba, ina fatan gudanar da ayyukan da suka shafi kasar Sin, don ba da gudummawa ga zumuncin dake tsakanin Sin da Brazil.