logo

HAUSA

AU ta amince da taswirar warware rikici a Sudan

2023-05-29 09:27:15 CMG Hausa

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta amince da taswirar warware rikicin kasar Sudan, a kokarin kawo karshen amon bindigogi a kasar.

Wata sanarwar da kungiyar ta fitar a jiya Lahadi ta bayyana cewa, an amince da taswirar ce a yayin taron kwamitin sulhu da zaman lafiya na kungiyar da aka gudanar a matakin shugabannin kasashe da na gwamnatoci a ranar Asabar, inda aka mai da hankali kan halin da ake ciki a Sudan.

Taswirar ta zayyana abubuwa guda shida, wadanda suka hada da kafa tsarin hadin gwiwa don tabbatar da cewa, an hade dukkan kokarin da masu fafutuka na yanki da na duniya suka yi ta yadda za su yi tasiri, da hanzarta dakatar da tashe-tashen hankula na din-din-din, mai ma’ana, da kuma ingantaccen mataki na jin kai.

Taron shugabannin ya jaddada muhimmancin samar da zaman lafiya guda daya, mai kunshe da dukkan sassan kasar Sudan, karkashin hadin gwiwar kungiyar AU, da kungiyar raya kasashe ta IGAD, da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa, da MDD, gami da abokan hulda masu irin wannan tunani. (Ibrahim)