logo

HAUSA

Gwamnatin tarayar Najeriya ta baiwa wasu `yan kasashen waje 385 shedar zama `yan kasa

2023-05-29 21:09:26 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta baiwa wasu `yan kasashen waje su 385 dake zaune a kasar takardar shedar zaman `yan kasa bayan tayi rijistar su .

A ranar asabar 27 ga wata tsohon shugaban tarayyar Najeriya da wa`adin aikin sa ya kare a yau litinin Muhammadu Buhari ne ya bayar da takardun shedar zama dan kasar yayin wani kwarya-kwaryar biki a birnin Abuja.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shugaban wanda tsohon mataimakin shugaban kasa Farfessa Yemi Osinbajo ya wakilta, yace bayar da takardar izinin zama `yan Najeriya da gwammati ta baiwa baki `yan kasashen waje wata mahimmiyar dama ce da masu zuba jari za su yi amfani da ita wajen sakewa domin saka jarin su tare kuma da bunkasa sha`anin yawon bude idanu.

Yace Najeriya a shirye take ta rinka bayar da kulawar gaske ga duk wasu baki mazauna kasar da suke da wata basira ta musamman wadda zata taimaki kasar wajen alkinta dimbin albarktun kasa da ake dasu musamman ma bangaren da suke da nasaba da makamashi.

Farfessa Yemi Osinbajo yayi marhabin ga ‘yan kasashen waje su 385 bisa kasancewar su cikin ‘yan Najeriya, inda ya tabbatar masu dacewa yanzu tarihi da al`adun Najeriya ya zama nasu .

Farfesa Yemi Osinbajo ya ce Yan Najeriya mutane ne masu masu kokari da juriya wajen neman na kan su, sannan kuma suna da kwarewa a fannoni daban- daban wadanda suka kunshi kimiya da fasaha, wannan ce ta sanya kasashen duniya ke kokarin amfana da irin basirar su.

“Haka kuma kamar yadda kuka sani ne Najeriya tana taka rawa sosai a kungiyar kasashen  nahiyar Afrika, muna yin duk abun da ya kamata dake nuna `yan uwantaka, mun jagoranci ayyukan wanzar da zaman lafiya a kasashe daban daban da suke cikin rikici a Nahiyar,duk wani dan Najeriya mu a wajen mu dane a kowacce kasa dake Nahiyar Afrika, Ina kira a gare ku, da ku ninka biyayyar ku ga kasa,tare da martaba manufofin kasa da kuma bin  dokokin kasa sau da kafa”

Yace Najeriya kasa ce dake maraba da duk wani bako daga kowacce nahiya ta duniya 

Daga cikin mutanen da suka samu dacewa da mallakar shedar zaman `yan Najeriya, sun hada da ‘yan kasashen Amurka, Labanon, Canada da Italiya.(Garba Abdullahi Bagwai)