logo

HAUSA

Hukumar zaben Turkiye ta ayyana Erdogan a matsayin wanda ya lashe zabe

2023-05-29 10:06:55 CMG Hausa

Shugaban majalisar koli mai kula da harkokin zabe a Turkiye Ahmet Yener, ya ayyana shugaba mai ci Recep Tayyip Erdogan, a matsayin wanda ya lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasar.

Ahmed Yener ya shaidawa manema labarai cewa, an sake zaben Erodgan a matsayin shugaban kasar Turkiye bisa sakamakon farko na zagaye na biyu na zaben.

Yener ya ce, Erdogan ya samu kashi 52.14 cikin 100 na kuri’un da aka kada a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar, yayin da abokin hamayyarsa Kemal Kilicdaroglu ya samu kashi 47.86 na kuri’un da aka kada.

Ya kara da cewa, an bude akwatunan zabe guda 196,744 wato kashi 99.43 na kidayan akwatunan zaben.

Jam’iyyar People's Alliance ta Erdogan, wadda ta kunshi jam’iyyar Justice and Development mai mulki, da jam’iyyar NMP, ta samu rinjayen kujeru 323 a cikin kujeru 600 na majalisar dokoki a zaben majalisar, yayin da jam’iyyun adawa guda 6, ta Nation Alliance suka samu kujeru 212.

Erdogan dai ya yi alkawarin cewa, idan aka zabe shi, zai kafa sabuwar Turkiye. Ya kuma jaddada shugabancinsa, a matsayin abin da ake bukata wajen samun daidaito a tsakanin hukumomin gwamnati da kuma zaman lafiyar kasar, kamar yadda kawancensa ke da rinjaye a majalisar dokokin kasar. (Ibrahim)