logo

HAUSA

Shugaban Nijar ya tattauna tare da mataimakin darektan zartarwa na SINOPEC

2023-05-28 16:38:29 CMG Hausa

Shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum ya tattauna a ranar Jumma’a 26 ga watan Mayun shekarar 2023 tare da mataimakin darektan zartarwa na kamfanin hakar man fetur na kasar Sin SINOPEC, mista Xue Weisong a fadar shugaban kasa da ke birnin Yamai.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

 

Shugaban kasar Nijar ya bayyana farin cikinsa bisa ga yarjejeniyar da aka sanya wa hannu tare da kamfanin SINOPEC, da shi ne kamfani mafi girma a duniya, in ji ministan man fetur din kasar Nijar Mahamane Sani Mahamadou, da ke cikin tawagar da ta gana tare da shugaba Mohamed Bazoum.

Ita dai wannan yarjejeniya ta shafi aikin hakar man fetur na zanguna da dama na man fetur a Nijar, sannan kuma muna nan muna nazarin hanyoyin da za su taimaka wajen bunkasa wani kamfanin harkokin man fetur cikin kasar mu, abin da ke zuwa daidai da hangen shugaban kasar Nijar, da ke da burin maida bangaren man fetur a matsayin wani ginshikin tattalin arzikinmu, ya kara da cewa.

Mataimakin babban manaja na SINOPEC ya nuna cewa yana cike da farin ciki matuka bisa ga sanya hannu kan wannan yarjejeniya da kuma ganin kamfaninsa zai halarta ga ci gaban tattalin arzikin Nijar.

Mista Xue Weisong ya bayyana cewa ta hanyar bunkasa bangaren kamfanin man fetur, muna fatan kara kyautata huldar abokantaka cikin girmama juna tsakanin Sin da Nijar da kuma kyautata jin dadin al’umomin kasashen biyu, ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa domin zama abin koyi ga sauran kasashen nahiyar Afrika.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.