logo

HAUSA

Tsohon shugaban kasar kenya ya shawarci shugaban tarayyar Najeriya mai jiran gado da yayi kokarin hada kan al`ummar kasar

2023-05-28 16:37:10 CMG Hausa

Tsohon shugaban kasar Kenya Uhuru Kanyatta ya shawarci shugaban tarayayar Najeriya mai jiran gado Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da ya yi kokarin yin duk wani abu da zai tabbatar da ginuwar kasar ba tare da la’akari da bambancin addini, jinsi ko siyasa ba.

Ya yi kiran ne jiya Asabar a birnin Abuja yayin taron lacca da Majalissar mika mulki ta shirya mai taken zurfafa harkokin demokradiyya domin hadin kai da cigaba.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Tsohon shugaban kasar ta Kenya ya ce sau tari yawan fadace-fadacen da ake samu a kasashe masu tasowa, yana faruwa ne sakamakon zakewa da wasu shugabanni ke nunawa wajen tara dukiya da fifita wata kabila ko addini.

Mr. Uhuru Kenyatta ya yi nuni da cewa, duk da cewa dai neman kuri’a kafin zabe na iya raba kan jama’a, to amma ya zama wajibi shugabannin su rungumi dabi’ar hada kan jama’a wanda ta hakan ne za su samu cimma burin su na gina kasa.

Tsohon shugaban kasar ta Kenya ya ci gaba da cewa, duk wani shugaba da ya samu nasarar zabe, babban aikin dake gaban sa shi ne sauya mummunan zaton da ‘yan hamayya ke yi masa kafin kasancewar sa shugaba.

Mr. Uhuru Kenyatta ya ce, ya zama dole ga shugabannin kasashen Afrika su rinka waiwayen halin da nahiyar ta shiga lokacin da turawan mulkin mallaka suka rarraba nahiyar zuwa shiyya-shiyya, wanda hakan ya haifar da matsalolin ga dorewar al’adun mu da yanayin zamantakewa.

Ya ce irin wannan tunani zai taimaka mana sosai wajen kara kishin cigaban kasashen mu ta fuskar tattalin arziki, siyasa da al’adu.

A kan sabon shugaba da mataimakin sa da za a rantsar a gobe Litinin, tsohon shugaban na Kenya ya ce yanzu kalubalen yakin neman zabe ya wuce, babban kalubalen dake gaban su shi ne kokarin tsara gwamnati da za ta nazarci matsalolin ‘yan Najeriya da nufin warware su.

Haka zalika Mr. Uhuru Kenyatta ya tunatar da sabon shugaban na Najeriya Bola Ahmad Tinubu.

“Nasarar ka yanzu ta wuce na batun kuri’u da aka kada maka kamar yadda tsarin demokradiyyar yammacin Turai yake. Nasara ta hakika yanzu ita ce ta yadda kowa zai ji dadi gwamnatin ka, ka yi kokarin tabbatar da ganin al’umomin dake kowanne sashe su fahimci cewa nasarar ka tasu ce, kuma gwamantin ka gwamntin su ce, manufofin ka kuma sun yi daidai da tunanin su, tare da kasancewar kasa daya gwamnati daya.”

“A mastayin ka na shugaba, dole ka yi kokarin fahimtar yadda za ka jagoranci mosaya da makiya da zuciya guda ba tare da ka nuna bambanci ba, domin yanzu a matsayin uba kake ga kowa”. (Garba Abdullahi Bagwai)