logo

HAUSA

Fadar White House Da Jam’iyyar Republicans Sun Cimma Matsaya Kan Yawan Bashin Da Amurka Za Ta Iya Karba

2023-05-28 16:24:06 CMG Hausa

 

Fadar White House ta kasar Amurka da Jam’iyyar Republicans sun cimma matsaya kan kara yawan bashin da kasar za ta iya karba domin kaucewa yuwuwar samun koma baya, yayin da ake tsaka da fama da rarrabuwar kai saboda siyasa a kasar da ma matsalolin duniya.

Cikin wata sanarwa a jiya, shugaba Joe Biden ya bayyana cewa, yarjejeniyar wani muhimmin mataki ne dake alamta sassanci.

Ya kara da cewa, nan da kwana guda, tawagar dake tsara yarjejeniyar za ta kammala tsara daftarin doka, inda za a gabatar da shi ga majalisun wakilai da na dattijai

Shi ma shugaban majalisar wakilan Amurka Kevin McCarthy, ya sanar da batun a shafinsa na sada zumunta.

A cewarsa, za a gabatar da yarjejeniyar ta adadin bashin da kasar za ta iya karba ga mambobin majalisar a yau Lahadi, kana a ranar Laraba su kada kuri’a kai.

A cewar sakatariyar baitulmalin Amurka Janet Yellen, idan har zuwa ranar 5 ga watan Yuni, majalisar ba ta kara yawan bashin ba, ko kuma ta dakatar da yarjejeniyar, to baitumalin ba zai samar da isasshen kudin da gwamnati ke bukata ba.

A cewar sashen aiwatar da bincike na majalisar wakilan Amurka, tun bayan yakin duniya na 2, an gyara matakin yawan bashin da Amurka za ta iya karba har sau 102. (Fa’iza)