logo

HAUSA

Gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da kamfanin jiragen sama mallakinta da aka dade ana dako

2023-05-27 17:41:12 CMG Hausa

Gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Nigeria Air mallakin kasar, wanda aka dade ana jira, wanda kuma ke zaman wani muhimmin ci gaba a bangare sufurin jiragen sama na kasar mafi yawan jama’a a Afrika.

Da yake gabatar da jirgin a filin jirgin saman kasa da kas ana Nnamdi Azikwe dake Abuja babban birnin kasar, ministan kula da sufurin sama na kasar, Hadi Sirika, ya ce manufar samar da kamfanin jiragen sama mallakin kasar ita ce, sake sanya kasar cikin muhimman masu ruwa da tsaki a kasuwar sufurin jiragen sama ta duniya.

Ministan ya ce ana sa ran kamfanin zai bunkasa bangaren sufurin sama na kasar da inganta ci gaban tattalin arziki da ma wakiltar misalin tsarin hadin gwiwar gwamnati da bangarori masu zaman kansu a tsakanin ‘yan kasuwar da gwamnatin kasar da ma abokan hadin gwiwarsu na kasar Habasha.

A cewar Hadi Sirika, kamfanin jiragen saman zai fara gudanar da zirga-zirga a cikin gida da kuma shiyya nan bada jimawa ba, yana mai cewa ana sa ran zai samar da guraben ayyukan yi 70,000 idan ya fara aiki gadan-gadan, sannan zai samar da jirage 30 cikin shekaru 5. (Fa’iza Mustapha)