logo

HAUSA

Shugaban Nijar ya gana da ministocin sufuri da kasuwancin kasashen Benin, Togo, Nijar da Burkina Faso a birnin Yamai

2023-05-27 17:01:13 CMG Hausa

Shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum ya gana a ranar Alhamis 25 ga wata tare da ministocin sufuri da kasuwanci na kasashen Benin, Burkina Faso, Nijar da Togo, da suka zo yi masa bayani kan sakamakon tattaunawar wani zaman taro da suka yi a birnin Yamai. Ko mene ne zaman taron ya maida hankali a kai ? Daga Yamai, abokin aikin mu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Shi dai wannan zaman taro ya maida hankali kan sanarwar bangarori hudu bisa aminintaccen tsari na sufuri cikin tsarin aiwatar da yankin cikin ‘yanci na musanya tsakanin nahiyar Afrika na ZLECAF, inji ministar kasuwancin kasar Benin, madam Assouman Alimatou Shadiya, bayan ganawarsu tare da shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum.

Tashoshin ruwa na Cotonou da Lome su ma na tamkar na Nijar da kuma Burkina Faso, ta kara da cewa, tare kuma da jaddada cewa daidai ne a samu jituwa cikin aiwatar da dokokin tafiyar da tsari a cikin kasashen hudu.

Wannan na kai mu da sake duba tsarin daidaita sufurin kayayyaki da kuma mutane, ta yadda za’a saukaka musanya da za ta taimakawa ga cigaban kasashen makwabta kuma ‘yan uwa, in ji madam Assouman Alimatou Shadiya.

Mun samu kwarin gwiwa daga wajen shugaban kasa mai girma Mohamed Bazoum, haka kuma ya samu goyon baya daga ‘yan uwansa kuma takwarorinsa na kasashen Benin, Togo da Burkina Faso, domin su bunkasa matakin duba alkibla guda, domin ganin kasuwanci ya kasance wata babbar hanyar samun kudin shiga da kuma kasancewa wani ginshikin cigaban kasashenmu, inji ministar kasuwanci da sufurin kasar Benin.