logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da sabon gidan yari mai cin mutane 3,000 a jihar Kano

2023-05-27 16:12:53 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon gidan yari mai cin mutane 3,000 a Janguza dake jihar Kano, irin sa na farko a yammacin Afrika.

Sabon gidan yarin wanda ya kasance mafi girma yanzu haka a Najeriya, an samar masa da kayayyakin zamani domin tabbatar da walwalar daurarru.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shi dai wannan gidan yari an fara gina shi ne a zangon farko na gwamnatin shugaba Buhari.

Da yake jawabin, shugaba Buhari ya ce gwamnati ta damu mutuka bisa yadda akasarin gidajen gyaran hali dake kasar suke a cunkushe sannan kuma akwai karancin ababen more rayuwa da suka hada da tsaftaccen ruwa da kayayyakin kiwon lafiya, lamarin dake mutukar barazana ga yanayin lafiyar daurarrun.

Shugaban kasar ya ci gaba da cewa sabon gidan gyaran halin na jihar Kano yana daya daga cikin guda shidda da ake ginawa a shiyyoyi 6 na kasar.

Shugaban na tarayyar Najeriya ya ce babu shakka sabon gidan yarin na Kano zai taimaka wajen rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa wajen jigilar masu laifi zuwa kotuna, kasancewar an samar da kotu a harabar gidan.

Shugaba Buhari ya yi fatan gwamnati mai zuwa za ta dora daga inda gwamnatin sa ta tsaya wajen kula da bangaren shari’ a da kuma kyautata yanayin rayuwar daurarru.

A jawabin sa, ministan harkokin cikin gida na tarayyar Najeriya Rauf Aregbesola kira ya yi ga gwamnatocin jahohi da su rinka daukar dawainiyar ciyar da mutanen da suka aikata laifi a jahohin su kuma ake tsare da su a gidajen gyaran hali mallakin gwamnatin tarayyar.

Yace bukatar hakan na kunshe cikin kundin tsarin mulkin kasar da aka yiwa kwaskwarima kwanan nan.

ACC Abubakar Umar shi ne babban jami`i mai magana da yawun hukumar lura da gidajen gyaran hali na tarayyar Najeriya yayi wa CRI Karin bayani game da sabon gidan gyaran halin na Kano

“Ana da kotuna har guda hudu da high court da kotun Majistare wanda ba za a iya samu a wani waje ba, ga asibitin mai dauke da gadaje 60 kuma akwai na’urorin sanyaya daki da kuma bangaren tiyata wanda suke da kayayyakin aiki irin na zamani, akwai bangaren motsa jiki daban daban da suka hada da filin kwallo, haka kuma an samar da jami’a wadda ake karatu daga gida, akwai kuma makarantar koyon sana’o’in hannu wanda idan sun kammala zaman gidan kason zasu iya fara gudanar da sana`ar dogaro da kai”

Ko wanne lokaci dai cikin watan gobe na Yuni za a fara kai wadanda aka yankewa hukuncin dauri gidan musamman daga jahohin dake shiyyar arewa maso yammacin Najeriya. (Garba Abdullahi Bagwai)